Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya cika shekaru 65: Abubuwan da ya kamata ku sani game da shi

31

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji (Dr) Muhammad Sa’ad Abubakar III, shi ne sarkin Musulmin Najeriya na 20 da ake ƙiyasta yawansu ya kai kimanin fiye da mutum miliyan 80.

Muhammad Sa’adu Abubakar ya zamo ɗaya daga cikin Musulmi 500 da suke da tasiri a duniya, sannan kuma a cikin waɗannan mutane 500, shi aka ɗauka ya zama na goma sha shida a cikinsu.

An haifi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dr) Muhammad Sa’ad Abubakar III a ranar 24 ga watan Agusta na shekarar 1956 a garin Sakkwato. Shi ɗa ne ga Sarkin Musulmi na 17, Saddiq Abubakar Usumanu wanda ya shafe shekaru fiye da hamsin akan karagar mulki.

Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi karatunsa na firmare a makarantar firmare ta ‘Sultan’s Ward Primary School’, da ke Sokoto. Bayan kammala firamare kuma sai ya shiga kwalejin Barewa (Barewa College) da ke Zaria.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar III

A shekarar 1975 ya samu shiga makarantar soja ta NDA (Nigerian Defence Academy) da ke Kaduna. Bayan kammala wannan karatu nasa, aka ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant) a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1977.

A ranar 2 ga watan Nuwanba ne dai Muhammad Sa’adu Abubakar ya gaji wansa marigayi Muhammadu Macciɗo Sultan na 19 wanda kuma ya rasu sakamakon wani hatsarin Jirgin saman kanfanin ADC jim kaɗan bayan tashinsa daga filin Jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III

Sultan Sa’adu ya shiga aikin Soji a shekarar 1975, kuma bayan ya kammala horon Sojin ne ya zama laftana wato mai anini ɗaya. Bayan wannan kuma Sarkin Musulmin ya halarci kwasa-kwasai a ciki da wajen Najeriya a ƙasashe da suka haɗa da Indiya da Kanada.

Bayan komowarsa gida ya zama kwamandan Sojojin Tankan Soji masu bada kariya ga shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1980. Bayan wannan kuma ya zama kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar OAU a Chadi. Har ila yau Sarkin Musulmin ya zama wakilin Soji na Najeriya a ƙungiyar Ecowas, bayan zama wakili a rundunar Sojin yammacin Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Saliyo.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da tsohon sakataren wajen ƙasar Amurka, John Kerry

Kafin naɗa shi Sarkin Musulmi na 20, Sa’adu Abubakar ya zama wakilin Sojin Najeriya a ofishin Jakadancin Najeriya a Pakistan. Kuma yanzu haka yana da matar Aure da kuma ‘ya’ya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan