Shekaru 52 Na Babagana Umara Zulum: Gwamnan da ya shafe shekaru 16 yana sana’ar tuƙin mota

25

Jama’a da dama sun yi shaidar Babagana kan cewa ba mutum ba ne wanda yake son kyalkyalin kayan duniya ko kuma tara makudan kudi, ganin irin damar da ya samu ta tara abin duniya a matakai daban-daban bayan ya sha gwagwarmayar rayuwa.

Babagana Umara Zulum a cikin ƴan gudun Hijira

A baya-bayan nan tauraruwar gwamnan na haskawa a Najeriya, inda ake yawan yabon sa da jajircewa da nuna tausayin talaka, musamman halin da mutanen jiharsa ke ciki sakamakon rikicin Boko Haram.

Takaitaccen Tarihin Gwamna Babagana Umara Zulum

An haife Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar 26 ga watan Agustan 1969 a karamar hukumar Mafa ta jihar Borno, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a garuruwan Mafa da Monguno tsakanin 1975 zuwa 1985.

Tun a lokacin da yake dan aji biyar a sakandare, Babagana ya bayar da himma wajen fara daukar nauyin karatunsa.

Domin haka ne ya shiga sana’ar tukin mota a 1984 inda ya shafe kusan shekaru 16 yana wannan aiki.

Gwamna Babagana Umara Zulum

Ya ci gaba da sana’ar tukin mota har ya je jami’a ya fara aikin gwamnati yana wannan sana’a.

Ya tuka mota nau’in tasi zuwa kirar bas da kuma a-kori-kura ta daukar itatuwa, kuma da tukin motar ne ya ci gaba da daukar nauyin karatunsa.

A shekarar 1986, Zulum ya samu gurbin karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat da ke Maiduguri domin karantar fasahar ban ruwa da noman rani.

Zulum na tafiyar kusan kilomita takwas daga Unguwar Kofa Biyu zuwa makaranta a duk lokacin da yake da aji.

Domin kara samun kudi don tallafa wa karatunsa, Babagana Zulum ya fara sana’ar markade a ranakun Asabar da Lahadi.

Gwamna Zulum ɗauke da buhunhunan abinci yana rabawa ƴan gudun hijira

Ya kammala karatunsa na difloma a 1988 inda kuma ya fara aiki a ma’aikatar noma ta jihar Borno tsakanin 1988 zuwa 1989, sa’annan ya koma hukumar kananan hukumomi ta Borno State Unified Local Government Service a jihar.

Duk da cewa ma’aikacin gwamnati ne a wancan lokaci, hakan bai hana shi tukin mota ba har zuwa lokacin da ya samu gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri domin karanta fasahar noma wadda ya kammala a 1994.

Saboda son ganin ya samu karatun boko ingantacce, ya tafi Jami’ar Ibadan inda ya yi digiransa na biyu kan fasahar noma.

Sai dai kafin fara digiri na biyu, sai da ya jinkirta rijistar zangon karatunsa inda ya dauki makonni uku domin yin kabu-kabu da mota domin samun kudin rijistar zangon karatun.

Ko da ya kammala karatun a 1998, ya dawo a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar a matakin babban injiniyan noma a jihar.

Ko a lokacin da ya dawo aikin gwamnati, ya fara koyarwa a Jami’ar Maiduguri kuma a wannan jami’a ce ya kammala digirinsa na uku kan kasa da fasahar ruwa ( Soil and Water Engineering) a shekarar 2009.

Muhimman abubuwa game da Gwamna Babagana Umara Zulum

  • Ya yi sana’ar saka tiles yana yaro karami tare da mahaifinsa.
  • Ya shafe shekaru 16 yana tukin mota a matsayin direban tasi da kuma daukar itace.
  • Ya yi sana’ar markade lokacin da yake karatun difiloma.
  • A lokacin da yake firamare, yana tafiyar kilomita bakwai zuwa makaranta.

Yaushe Gwamna Babagana Umara Zulum Ya Fara Siyasa?

Ganin irin jajircewar Babagana da kuma tsawon tarihin da ya kafa kokari a wajen aiki da kuma rike gaskiya, tsohon gwamnan Borno a wancan lokaci Kashim Shettima ya zabi Babagana domin ya zama shugaban kwalejin kimiyya ta Ramat.

Sai dai ko a lokacin da aka ba shi wannan mukami, Farfesa Babagana ya shaida cewa ba zai karbi wani albashi ba a matsayin shugaban jami’a, zai ci gaba da karbar albashinsa a matsayinsa na malamin makaranta.

Gwamna Kashim Shettima ya ba shi kwamishina mai lura da sake gina yankin da Boko Haram suka lalata, saboda nagartarsa da ya gani.

Tun daga wannan lokaci Zulum ya dukufa da aikin da ya rataya a wuyansa har kuma ya samu nasarar sa ido wajen gina dubban gidaje da za su kwashi dubban ‘yan gudun hijira.

Ko a lokacin da jam’iyyar APC ta ayyana Babagana Umara Zulum a matsayin wanda zai tsaya takararta ta gwamna a 2019, ya riga ya yi suna a jihar ta Borno bisa tarihin da ya kafa na jajircewa wajen aiki da rikon amana.

Jarumtar Gwamna Babagana Umara Zulum

Jarumta da ƙoƙarin ganin ya kyautatawa talakwan jihar Borno, wannan ce ta sanya Gwamna Zulum ɗin ke shiga gurare masu hadarin gaske wanda ma ake ganin matattarar ƴan ta’addar Boko Haram ce.

Haka kuma a wata tattaunawa da BBC Hausa da Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ya bayyana cewa ba ya tsoron mutuwa shi ya sa yake shiga duk wurin da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suke zaune.

Da aka tambaye shi kan dalilin da ya sa yake zuwa yankuna masu hatsari wadanda aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram, har ma yakan kwana, sai Gwamna Zulumm ya ce “mutane su gane cewa raina sai lokacin da Allah ya ce zai fita sannan zai fita.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan