Fitila: Manyan Rahotannin Makon Jiya Da Ya Kamata Ku Karanta

20
Ali Sabo

A wani babban al’amari mai kama da almara, a daren ranar litinin din data gabata ne aka sami labarin cewa yan bindiga dadi sun kai hari makarantar horar da sojojin Najeriya wacce ake kira NDA

A harin da yan bindigar suka kai an samu labarin asarar rayuka na sojoji guda biyu sannan kuma anyi garkuwa da wani mai mukamin mejo wanda daga bisani aka sami labarin mutuwarsa.

Wannan gagarumin hari dai da ya dugunzuma jama’a sannna ya haifar da razani a zukatun al’umma ganin irin girman gurin da ‘yan bindigar suka kai harin. Masana harkokin tsaro da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun tofa albarkacin bakinsu game da harin da aka kai. Masanan wadanda sun dade suna kiraye-kiraye ga gwamnati kan ta tashi tsaye ta dauki mataki kafin abin yafi karfin ta suna ganin dai yanzu al’amarin ya gagari kwandila.

Dalilin wannan batu dai shi ne idan muka yi duba da matsayi da kuma tsaron dake wannan wuri zamu fahimci cewa lalle yan bindigar sunyi wani karfi da ke nema ya gagari gwamnati.

Ku Karanta: Fitila: Manyan Rahotannin Da Yan Jarida Suka Rawaito A Makon jiya

Ga wadanda ba su san wannan wuri ba, ita dai NDA ita ce makarantar da ake horar da dukkanin wasu manyan jami’an tsaro na soja kama daga sojan kasa, sojan sama da kuma na ruwa, sannan wannan wuri zamu iya cewa in aka dauke fadar shugaban kasa, guraren da suka fi wurin tsaro da kuma jami’an tsaro a kasar nan ba su da yawa.

To tambaya a nan shi ne ta yaya aka bari har wadannan yan bindigar suka kai hari wannan wuri, sannan suka yi garkuwa da babban jami’in soja?

To amma masu biyayyar al’amarin tsaro wannan ba zai zo musu a bazata ba lura da yadda a baya aka rinka bawa jami’an tsaron shawara na cewa su tabbata sun dauki mataki mai tsauri kan wadanda suka kashe wani babban jami’in sojojin mai mukamin Janar wanda ake kira da Janar Alkali amma suka gaza.

Idan mukayi duba da maganar gwamnan jihar Katsina wato Aminu Bello Masari wanda yake cewa al’umma ya kamata su tashi tsaye su kare kansu akan hare-haren da yan bindiga suke yi duk da dai gwamnatin tarayya ta ce maganar ba ta kamata ba, amma duba da abubuwan da suke faruwa a yan kwanakin nan kwarai talaka sai dai ya tashi ya kare kansa domin jami’an tsaro abin ya fara gagarar su.

Haka kuma, rahoton da ke fitowa daga jihar Zamfara, na nuni da cewa yan majilasar jihar sun kauracewa zaman da suka saba yi saboda gazawar gwamnati na ceto mahaifin kakakin majalisar jahar. Wanda idan zamu iya tunawa, a kwanakin baya ne yan bindiga suka yi awon gaba da mahaifin kakakin majallisar.

Amma abinda yake daurewa al’umma da masu fashin baki kai shi ne, yadda a baya yan majalisar duk da rashin tsaron da ake fama da shi a jihar basu taba daukar mataki irin wannan ba sai a wannan lokaci. Wannan mataki nasu ya nuna karara cewa mahukunta a kasar nan bata al’umma suke yi ba, kawai suna kare maradunsu ne da kuma na iyalansa.

Mai tambaya zai yi tambaya yace wanne mataki yan majalisar suka dauka akan sace-sacen mutanen da ake yi a jihar, wanda ko a makon da ya gabata sai da aka dauke yan makarantar koyan aikin gona na Bakura. Duk mai hankali yasan basu da wata amsa sai son rai kawai.

Jihar Plateau, wacce tayi kamari da kaurin suna wurin tashe-tashen hankula a wannan makon da muka yi ban kwana da shi an sake samun rahoton rikici a wannan jiha in da aka samu asarar rayuka wanda bai gaza na mutune talatin ba. Ko a makon da ya gabata Labarai24.com ta kawo muku rahoton yadda wasu yan ta’adda suka halaka wasu matafiya yan jihar Osun akan hanyar su ta koma gida. Gwamnatin jihar tuni dai ta sanya dokar kulle na awanni ashirin da hudu a jahar.

Sai dai a wasu rahotani da suke fitowa daga jihar suna nuni da cewa al’umma da dama sunyi zanga zanga inda suke kira da gwamnan jihar da ya sauka daga mukaminsa domin ya gaza a wurin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Irin wadannan kiranye-kiranye dai an dade ana yin su a wannan kasa inda al’ummar suke ta kira ga shuwaganni da su sauka daga mukaman su domin sun gaza kare al’umma. Idan zamu iya tunawa dai ko a baya irin wadannan kiranye-kiranye ne suka sa aka sauke shuwagabannin hafsoshin sojojin kasar saboda gazawa.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya fito ya nemi gwamnatin tarayya da ta aiyana dokar ta baci a jihar bayan da aka fitar da sanarwa cewa sama da kauyuka saba’in sun koma hannun yan bindigar dake yankin. Wannan kira nashi ba wani abin mamaki ba ne ga masu bin al’amura don tuntuni ake kira ga shugaban kasa akan hakan.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Amma dai abin tambaya anan shi ne, ya kamata gwamnatin tarayya ta matsa shi gwamnan domin yayi mata bayani game da wasu kalamai da ya taba yi a baya na cewa idan ya fidda sunayen mutanen da suke da hannu akan harkar fashin daji da garkuwa da mutane sai an sha mamaki

Wannan batu na Janar Alkali da sauran kisan gilla da ake yiwa sojojin kasar nan sannan ba’a daukar wasu matakai masu tsauri suna daya daga cikin abubuwan da suke sanya yan bindigar suke cigaba da cin karensu babu babbaka. Kuma in har dai gwamnati ba zata tashi tsaye akan al’amarin ba to lalle za a dade kafin ayi maganin wannan masifa.

Lititoci masu neman kwarewa a Najeriya sun shiga mako na hudu da yajin aikin da suka fara game da kin biyan su hakkokinsu da gwamnatin tarayya tayi. Tun kafin tafiyar tasu yajin aikin sun bawa gwamnati wa’adi na gargadi kan ta tabbata ta cika alkawarrukan da suka yi a shekarar dubu biyu da sha tara amma hakan bai samu ba, inda likitocin suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Asibiti

Wannan yajin aiki dai ya mayar da harkokin lafiya a kasar nan baya wanda dama yana cikin mashasshara, ya saka al’umma musamman talakawa a cikin halin kaka-na-kayi. Hakan ya haifar da musayar yawu tsakanin likitocin da hukumar kwadago inda ministan kwadagon yayi barazanar dakatar da albashin duk likitocin da suka kauracewa bakin aikin su, sannan daga baya kuma gwamnatin ta shigar da kara a babbar kotun dake birnin tarayya Abuja.

A umarnin kotun da ta bayar, ta umarci likitocin da su koma bakin aikinsu. To koma dai menene wannan rikici dai talaka kawai yake shafa, in muka yi duba da cewa su wadannan masu mulkin da yawansu ba sa zuwa wadannan asibitoci na gwamnati wasu ma daga cikinsu kasashen waje suke zuwa kamar Amurka, da Dubai, da Birtaniya da Jamus inda suke barin talakawa a halin ni ya su.

Wannan dai ana ganin shi ne babban makasudin da ya sa mahukuntan basa mai da hanlkali akan duk wani abu da ya shafi talaka. Kiran mu dai anan shi ne ya kamata dukkanin bangarorin suyi duba na tsanaki, sannan su yiwa talaka adalci don shi ne yake shiga halin tsaka mai wuya.

Kasasashen Waje

Har yanzu ana cigaba da tata burza a kasar Afghanistan inda ake misayar yawu tsakanin shuwagabannin Taliban da kuma kasar Amurka. A makon da ya gabata ne dai kasar Jamus ta fitar da sanarwa cewa ba zai yiyu a iya debe dukkanin mutanen da ake son debewa zuwa kwanakin da akayi yarjejjeniya da shuwagabannin Taliban ba.

Shugaban Amurka Joe Biden

Sai dai shugabannin Taliban din tuni suka fitar da sanarwar cewa ba zasu kara wa’adin da akayi alkawari a baya ba, kuma idan sojojin Amurka da kawayen ta basu fita daga kasar ba zuwa wannan lokacin duk abinda ya faru kar su zargi kowa su zargi kansu. Amma dai tuni kasar Amurka ta fitar da sanarwar cewa zasu gama kwashe duk mutanen kafin lokacin.

Haka ma kuma a ranar Alhamis an sami labarin tashin bama-bamai a filin jirgin tashin jirage na Hamid Karzai dake Birnin Kabul, inda rahoton da gidan talabijin na Aljazeera ya fitar na nuni da cewa sama da mutum sittin tare da dakarun Amurka goma sha biyu sun rasa rayukansu.

Ku Karanta: Abin Mamaki: Cikin Tsofaffin Birane 22 Da Suka Wanzu A Afrika Har Da Kano

Tuni dai kungiyar yan ta da kayar baya wacce ake kira da Islamic State of Iraq and Levant (ISIL) suka dauki alhakin kai harin. Wannan hari dai ana gani zai iya mayar da yarjejjeniyar kwashe dakurun Amurka baya a wannan kasa ta Afghanistan.

Wannan batu dai na Afghanistan abu ne mai matukar daukar hankali kuma ya mayar da hankalin duniya musamman manyan kasashe masu kare hakkin mata da bil’adama wannan kasa.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan