Gwagwarmaya da tarihin Sule Lamiɗo a shekaru 73: Abubuwan da ya kamata ku sani

  27

  Shi ne gwamnan Jihar Jigawa na shida sannan kuma gwamnan farar hula na uku. Alhaji Sule Lamiɗo, gogaggen ɗan siyasa ne, wanda ya fara siyasa tun a zamanin PRP ta Marigayi Malam Aminu Kano wanda a hannunsa ya koyi siyasa. Ya haura shekaru 35 yana siyasa.

  An haifi Sule Lamiɗo a ranar 30 ga watan Agustan shekarar 1948 kimanin shekaru 73 da su ka gabata a garin Bamaina ta cikin ƙaramar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa. Ya yi karatu a ‘Senior Primary School Birnin Kudu’ wacce yanzu ta koma ‘Government College, Birnin Kudu), daga nan kuma ya wuce zuwa Kwalejin Barewa ta Zariya (Barewa College, Zaria).

  Ya riƙe muƙaman siyasa da dama, tun daga PRP, SDP, har zuwa jama’iyyarsa ta yanzu wato PDP. An taɓa zaɓensa a matsayin wakili a zauren majalisar wakilai ta Najeriya (Member Federal House of Representatives) a jamhuriyya ta biyu, sannan kuma ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Waje na Najeriya a lokacin shugaba Olesegun Obasanjo.

  Dakta Sule Lamido CON

  Ya zama gwamnan jihar Jigawa a shekarar 2007 bayan ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2007 ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP. Haka nan kuma aka sake zaɓensa a karo na biyu a watan Afirilu na shekarar 2011 bayan cikar wa’adin mulkinsa na farko.

  Sule Lamido Gudunmawa da ya bayar wajen haɓɓaka jihar Jigawa tana da wahalar ƙididdiguwa, shi ne ya gina katafariyar sakatariyar jihar (State Secretariat) da ke Dutse, shi ya gina gidan radiyo da talabijin na Jigawa, shi ya samar da filin sauka da tashin jiragen sama na Jigawa, shi ya samar da Jami’ar jihar Jigawa da ke ƙaramar hukumar Kafin Hausa, shi ya samar da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Jigawa da ke Dutse, shi ya gina kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Birnin Kudu, shi ya gina gidajen ƙanan hukumomi 27 da ke Dutse, shi ya gina gidajen saukar manyan baƙi (G9) na Jigawa da ke Dutse, da sauran ayyuka masu tarin yawa.

  Ya bar wannan kujera ta gwamnan jihar Jigawa bayan cikar wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya damƙa ragamar mulkin a hannun Alhaji Badaru Umar Ɓaɓura a shekarar 2015.

  Bayan barinsa gwamnan Jigawa a shekarar 2015 hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin aziki zagon ƙasa, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan tare da ‘ya’yansa biyu da kuma wani mutum a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano Karkashin mai shari’a justice Evelyn Anyadige.

  Hukumar ta EFCC ta ce ta gurfanar da Sule Lamido a gaban kuliya ne bisa zargin sama-da-faɗi da makuden kudade a lokacin mulkinsa.

  Inda kotun ta aike da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido kurkuku kafin a cigaba da shari’a.

  Sule Lamido, yana daya daga cikin jigajigan ƴaƴan babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, kuma ya yi fice wajen sukar irin kamun ludayin gwamnatin jam’iyyar APC.

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan