Saukale na bazata akan ministan harkokin noma da na lantarki

  22
  Sabo Nanono

  Dazu shugaban kasa Muhammad Buhari ya sallami manomi dan shekara 74 daga mukamin minista. Haka kuma an yi wa ministan wutar lantarki ritaya ta dole.

  Haka al’adar mukami na nadi take. Kana zauna ba shiri za a koreka, ba kuma za a baka notis ba. Duk wanda aka nada a mukamin siyasa dole ya rika kwana da sanin haka.

  Tsohon Ministan Harkokin Noma Malam Sabo Nanono

  Saleh Mamman ya tafi. Jihar Taraba sai a shiga laluben madadi. Baba Nanono Allah ya kawo babban rabo. In Kanawa sun matsa kora a sake basu wata kujerar. In ba rabonsu, Nanono ya ci da rabonsu.

  Na samu cikakkun dalilan da PMB ya dogara da su ya sallami wadannan ministoci, kuma ya saka dan yana albishir cewa wasu MA za a basu takardar sallama.

  Allah ya sa da gaske ne. Tuntuni ya dace a baiwa NSA Munguno jan kati, kuma a hada shi da Janar Magashi. Tsaron kasar nan a wuyansu yake kuma baya ake ci ba gaba ba. Shi kansa gwamnan babban banki Godwin Emeifele son zuciya ne ke rike da shi. Lalacewar tattalin arziki yana da katon kamasho. Haka rashin bibiyar da zaman dirshan ne ya sanya su Burutai suka rika yadda suka ga dama, da yake ‘yan lele ne, bayan an kore su kuma aka basu manyan mukamai masu kariya.

  Tsohon Ministan Lantarki Sale Mamman

  Idan awo za a yi na gaskiya shi kansa mai gida Baba ma hutar da shi za a yi, a fara gwada Farfesa na Oladipo a ragowar shekara biyu. Zamu fi jin dadin awo a Fabrairu 2023.

  Naji mutane suna ta cewa ya kamata a saka matashi kar a guraben. Tuni na dawo daga rakiyar wannan tunanin. Abin da muke nema namiji ko mace mai tsananin kishin Najeriya. Mai niyyar kwarai. Mai kaifin tunani. Mai hakuri. Wanda ‘yan Najeriya ne a gabansa, ba APC da PDP da Buhari ba.

  WANNAN SAUKALEN YA YI MIN DADI. Dalili da ana yin haka da wasu lamuran ba su ta’azzara ba.

  Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan