Fitila: Tankade Da Rairayar Rahotannin Yan Jarida A Makon Jiya

31
Ali Sabo

Ku gaffarace ni, wannan makon a cikin fushi da bacin rai nake, kamar kowanne mako labarun da suka fi daukar hankali a wannan yanki namu na Arewacin Najeriya sune wadanda suka shafi tsaro.

A makwon da ya gabata ne aka sami labarin sace wasu mata guda biyu a garin Zaria wato Safina da Pharmacist Hannatu, abin takaicin a wannan labari shi ne, ita Hannatu wacce tuni aka sami labarin samun gawarta, kuma shaidun gani da ido suka tabbatar anyi mata kisan gilla ta hanyar harbi har sau uku a jikinta.

Babban abin takaici da tausayi game da kisan wannan baiwar Allah shi ne, ita dai marigayiyar da wadannan mutane marasa imani suka yiwa kisan gilla ta kasance tana dauke da juna biyu kamar yadda yan uwanta suka labartawa maneme labarai.

Rahoto Fitila na Makon jiya: Fitila: Manyan Rahotannin Makon Jiya Da Ya Kamata Ku Karanta

A rahotannin da ba’a tabbatar da ingancinsu ba, suna nuni da cewa dalilin harbin wannan mata shi ne yan bindigar sun bukaci da wadanda suka yi garkuwa da su din suyi gudu inda marigayiyar ta bada uzurin cewa tana dauke da juna biyu bazata iya gudu ba, dalilin haka yan bindigar nan take suka harbe ta har sau uku. Muna addu’ar Allah yaji kanta da rahma su kuma Allah ubangiji ya wulakanta su.

Haka kuma jahohin Kaduna, Katsina da Zamfara a makon da mukayi ban kwana da shi suka sanya dokar ta baci a jahohinsu wadanda suka hada da hana cin kasuwannin mako-mako, hana sayar da man fetur a kan tituna da kuma a cikin jarkoki, ka’idance adadin man fetur din da mutum daya zai iya saya wanda bai wuce na Naira dubu goma ba, da daidai sauran wasu sharruda.

To ko shin wadannan dokiki za su haifar da da mai ido koko a’a. Masana sunyi ta tsokaci akan wannan batu inda suke ganin wadannan dokoki kawai zasu kara rura wutar rikicin da ake fama da ita ne da kuma jefa al’ummomin yankunan cikin tsanin talauci da kunci fiye da yadda suke ciki a da.

Idan muka yi duba da cewa tun kafin wadannan dokoki al’ummomin wannan yankuna suna cikin tsananin talauci saboda da rashin aiyukanyi da suka yi karanci a wadannan yankuna, sai kuma gashi anzo dan abinda ya rage musu na neman abinci suma an haramta su. Masana dai na ganin cewa kamata yayi gwabnati kawai ta tashi tsaye inda gaske take ta magance wadannan matsaloli amma ba hana al’umma yin aiyukan da zasi kawo musu abun sawa a baki ba.

Kuna iya duba: Bama goyon bayan katse layukan sadarwa a Arewacin Najeriya – Dattawan Arewa

Sai gashi kuwa ba’aje ko ina da saka wadannan dokoki a jahohin ba, a jihar Zamfara a ranar Larabar da ta gabata aka sami labarin yin garkuwa da daliban babbar makarantar sakandiren jeka ka dawo na garin Kaya dake karamar hukumar Maradun inda daga nan ne gwamnan jihar wato Bello Matawelle ya fito su 73, a cewar rundunar yan sandan jahar.

Irin wadannan batu suna daga cikin abubuwan da ya sa masana musamman a fannin harkokin tsaro suke ganin cewa wadannan dokoki da aka saka a wadanan jahohi ba abunda zasu haifar illa kara jefa al’ummar wadannan yankuna cikin kangin talauci da rudani na rayuwa, sannan su kuma yan bindigar zasu cigaba da cin karensu babu babbaka tunda dama can suna da hanyoyin da suke samun makamansu da kuma man fetur da suke anfani dashi.

Sai kuma wani babban labari da ya yamutsa hazo a jaridun Najeriya musamman kafafen sada zumunta na zamani wanda a ranar talatar da ta gabata aka fitar da sanarwar shugaban kasa Muhammad Buhari ya sallami ministocinsa guda biyu, wato Sabo Nanono wadda sh ine babban ministan harkokn noma na kasar da Engineer Sale Mamman mai kula da hukumar wutar lantarki.

Sabo Nanono
Engineer Sale Mamman da Sabo Nanono

Korar wadannan ministoci dai ta haifar da cece-kuce a cikin al’umma inda jama’a da dama suka bayyana mabanbantan ra’ayoyi dangane da dalilan daya sa aka sauke ministocin. Kaso mafi yawa daga cikin al’umma suna ganin an kori ministocin ne saboda gaza sauke nauyin da ka dora musu, sai dai fadar shugaban kasa har ya zuwa yanzu bata fitar da wani takamaiman dalili na korar ministocin ba illa dai ta fitar da sanarwar cewa anyi hakan ne don kawo sauye-sauye a gwamnatin kuma za’aci gaba da hakan.

Sai dai babban abinda za’a fi tunuwa game da wadannan ministoci a wannan kasa shi ne, Alhaji Sabo Nanono shi ne ministan da ana tsaka da tsadar rayuwa da hauhawan kayan masarufi ya fitar da wata sanarwa inda yace a Najeriya dan kasa zai iya cin abincin na naira talatin kuma ya koshi, inda wannan batu ya haifar masa da suka ta bangoriri da dama.

Sai kuma a kwanakin baya inda ya kara fitar da sanarwar cewa yanzu abinci ya wadata a kasa Najeriya, shi ma a lokacin da abinci yake wahalar samu da kuma tsada.

Shi kuwa Engineer Mamman al’ummar wannan kasa zasu fi tunawa da shi ne a lokacin da aka nada shi minista inda ya kai wata ziyarar gani da ido a wata tashar wutar lantarki dake Mambila wacce tsohon ministan ma’aikatar wato Baba Raji Fashola yace an kusa kammala aikinta, amma shi Enginer Sale Mamman yace ko share wurin ba’a fara ba. Sannan yan kasa zasu tuna wannan minsitan da kare-karen kudin wutar lantarki duk da al’umma basa samun wutar.

A wani labari dake fitowa daga jihar Kano, a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka cigaba da zaman kotu wadda ake tuhumar Malamin addinin musuluncin nan wato Sheik Abduljabar Nasiru Kabara akan cin zarafin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), in zamu iya tunawa dai a zaman kotun daya gabata lauyoyin gwabnati sun bukaci da alkalin kotun shari’ar musulunci dake Tudun Maliki wato mai shari’a Sarki Yalo da ya sahale musu su karanto karin wasu tuhume-tuhume da suke yiwa shi Malamim inda lauyoyinsa suka ki amincewa dayin hakan, daga nan ne aka dage karar.

Sai dai a zaman kotun na ranar Alhamis mai shari’ar ya sahale musu dan su karanto karin tuhume-tuhumen nasu. Lauyoyin gwabnatin sun karanto wasu sababbin tuhume-tuhume guda hudu, amma ko da aka karanto masa tuhume-tuhumen Malamin yaki yace komai. Inda a nan ne mai shari’ar ya bukaci da akai wanda ake zargin asibiti domin a duba lafiyar kwakwalwarsa.

Abduljabar Nasiru Kabara

Daga nan sai lauyoyin Malamin suka bukaci da a basu kwafin karar domin su daga karar zuwa wata kotun.

Wannan batu dai na Sheik Abduljabar ya dade yana tayar da kura a jihar kano da wasu sassa na Arewacin Najeriya inda wasu suke ganin Malamin ya aikata mummunan laifi da ya kamata a yanke masa hukucin mai tsanani inda a hannu guda kuma wadansu suke gani bai aikata laifin da ake zarginsa ba, illa dai kawai ana so a hana shi wa’azi ne da kuma son a ci mutancinsa, wanda hakan yasa kwanakin baya wasu shakikan malamin suka aikewa da shugaban kasa wata budaddiyar wasika suke neman da ya shigo cikin lamarin malamin, tare da zargin wasu malamai da manyan mutane a garin Kano akan tuhumar da akeyi masa.

Yau ma nan zamu jingine wannan batu, za kuma mu cigaba da biyayya.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan