Abin da ya kamata jihohin Arewacin Najeriya su yi domin kaucewa faɗawa cikin talauci

  49

  Lokaci yayi da jihohin arewa zasu gane cewa, Nijeriya ba zata ci gaba da kasancewa yadda take ba a yanzu haka. Jihohi za su ci gaba da neman karin cin gashinkansu. Jihohi masu arziki kamar Lagos da Rivers zasu ci gaba da neman su samu karin iko; da karin kudin shiga da kuma yin dokoki da zasu tallafawa jihohinsu. Me ya kamata jihohin arewa su yi domin kaucewa fadawa cikin talauci da zama cima zaune a sha’anin Nijeriya?

  — Kowacce jiha ta tashi tsaye wajen bunkasa kasuwanci, noma da kiwo da kuma sauran hanyoyin samar da aikin yi da karin kudin shiga.

  —Kowacce jiha ta kara bude sabbin hanyoyin samun kudin shiga na cikin gida, ta hanyar haraji da sauran hanyoyi na bunkasa kudin shiga.

  —A kara karfi wajen samar da ilimi ga kowa. A karfafa yin ilimin zamani da kuma kara shiga fannin kimiyya (science) da fasaha (technology).

  —A rage gaba da yawan fada da zubar da jini da hayaniya da sunan addini. Nuna gaba da kiyayya saboda bambancin addini ko akida ba zasu amfani kowa ba. Mu sani ba yadda za a yi wani ya bi addininka ko akidarka saboda yadda kake ganin shi ba akan hanya yake ba, haka shima yake ganin kai ma akan bata kake.

  Malam Isa Sanusi

  —Malaman addini su maida hankali wajen hada kan jama’a da yin wa’azi akai-akai akan muhimmancin rike amana da tausayawa juna, da neman ilimin zamani da kuma koyon sana’a.

  —A tabbatar mata sun samu ilimi, kuma su koyi sana’a ta yadda idan ma basu da mai kula dasu zasu iya dogaro da kai ba tare da sun shiga wani hali ba.

  —Dole sai an rage yawan haihuwa barkatai, musamman ga wadanda basu da wadatar yin reino da kuma bada ilimi ga yara har su zama mutanen kirki. Haihuwar yara barkatai da kuma tura su yawon bara zalunci ne da kuma cin amana; domin kuwa haihuwa amana ce daga Allah.

  Malam Isa Sanusi, shi ne Mai magana da yawun ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya, ya rubuto daga Abuja

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan