Hannunka Mai Sanda: Nan gaba kaɗan ƴan Arewa za su zama bayi – Salihu Tanko Yakasai

  197

  Wato na ga alama da wasa da wasa nan gaba ɗan arewa sai an wayi gari ya zama bawa a ƙasar nan saboda rashin kishi da sanin madafar aiki da hangen nesa na shugabannin arewa da ma mu kan mu ƴan arewan.

  A wannan makon, gwamnan jihar Rivers wato Wike yayi nasara a wata kotu kan maganar karbar kudin haraji na VAT mai makon gwamnatin taraiya (ta hannun FIRS) ta karba a jihar sa, wannan mataki shi ma yana dab da zama doka a jihar Lagos, wanda suma jihar ce zata karbi wannan kudi ba gwamnatin taraiya ba, abinda wannan yake nufi shine idan jihohin kudu wanda su suka fi tara kudin haraji na VAT suka daina bari gwamnatin taraiya ta na karba, kenan za’a wayi gari kudin da jihohin arewa suke samu daga Abuja wato allocation zai yi kasa sosai, wanda mafi yawancin su kenan zasu durkushe domin a yanzu ma haka kusan kudin da suke samu ko albashi baya iya biya bare suyi aiki da shi. Wannan lamari ko da zai yi wuyar aiwatar wa, ni ina kallan sa a matsayin abinda ya kamata ya tashi arewa daga bacci.

  Salihu Tanko Yakasai

  Idan aka zo maganar kuɗaɗen shiga ban da jihar Kaduna da kuma Kano, ba wata jiha a arewa da take tara kuɗi sosai wanda zai sa ta dogara da kanta ba sai ta jira kuɗin Abuja ba. Duk da dai a kudancin ƙasar nan kamfanunnika sun fi yawa idan aka haɗa da na arewacin ƙasar, amma muna da hanyoyin da zamu inganta kuɗaɗen shigar mu, domin samun damar tsayawa da kafafun mu.

  Mafi ƙarancin misali, banga dalilin da za mu dinga dibar kayan abinci haka zalla muna kaiwa kudu ba, bacin zamu iya samar da kamfanin da zai gyara su ya sa a kwalli a kai shi kudun, wanda yin hakan sai ya fi daraja. Ko kuma a ce wai an ɗora shanu a mota an kai Kudu ba cin zamu iya yin abattoir, ya zamo cewa yankakken nama za a kai musu, idan kuma suna san saniya ko rago mai rai, to a zabga haraji yadda sai sun gwammace su sai yankakken. Yajin aikin kai albasa Kudu kawai arewa ta yi kwanaki amma sai da Kudu ta girgiza. Yin haka zai samar da aikin yi, da kudin shiga ga arewacin Najeriya saboda abinci ne arzikin mu. Shekara da shekaru an gagara yin kamfanin tumatirin gwangwani kwaya daya tak a Kano, wanda da an yi da manoman timatir sun rage asara ba kaɗan ba, kuma da tattalin arzikin su ya inganta.

  Duk bankunan da suke Kano, ko arewa ma gaba ɗaya, da kuma rassan manyan kamfanunnika zaka ga motocin su lambobin Lagos ne da su, su zo Kano mu tara musu kudi amma duk kudin harajin su Lagos yake komawa. A kan me?

  Shekara shida dan arewa na shugabancin ƙasar nan amma har yanzu arewa ba ta samu wutar lantarki ba wanda zai farfado da masana’antu a yankin mu, bare tattalin arzikin mu ya bunkasa, gashi wankin hula ya kai mu dare. Mun ci sa’a ma ana aikin bututun iskar gas wato AKK, wanda hakan zai sa a samu farfadowar kamfanunnika musamman a Kano da Kaduna, amma shi ma akwai sauran aiki a gaba.

  To gaskiya ina kira da babbar murya manyan mu da shugabannin mu da mu kan mu magoya baya, da a tashi tsaye, tsayin daka. Ya zama wajibi mu nemi hanyoyin da zamu inganta tattalin arzikin arewa yadda zamu iya tsayawa da kafafun mu, ko kuma mu zama bayi a ƙasar nan. Kowanne gwamna ya tabbatar kujera mafi kusanci da shi, da kuma wadda tafi kowacce muhimmanci ita ce kujerar kwamishina ko mai bada shawara akan fannin tattalin arziki. Sannan shugabannin arewa su dinga haduwa suna hada karfi da karfe wajen ganin sun ciyar da yankin mu gaba, ba suyi ta fada a tsakanin su ba, wannan ba ya shiri da wancan, wancan baya ga miciji da wannan. A duba halin da muke ciki, a cece mu tun kafin mu azabta.

  Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan