Ƙungiyar Sarakunan Fawa ta ƙasa ta karrama mataimakin gwannan jihar Kano

88

Hadaddiyar ƙungiyar Sarakunan Fawa ta ƙasa reshen arewacin Najeriya sun karrama mataimakin gwamnan jihar Kano kuma kwamishinan ma’aikatar gona ta jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da lambar yabo ta musamman.

Mataimakin Gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna

A lokacin taron Sarkin Fawan Sarkin Musulmi Alhaji Sada Musa Sokoto, ya bayyana cewa jajircewa da nuna kauna da kuma son cigaban sana’ar fawa a jihar Kano, ya sanya su ka karrama Nasiru Gawunan da kuma wasu fitattun mutane.

Wani Bangaren na mahalarta taron

Ya ƙara da cewa kungiyar ta su ta kan shirya irin wannan taron a jihohi daban daban da ke arewacin ƙasar nan. Kuma taron a jihar Zamfara ya kamata su yi amma sakamakon yanayin matsalar tsaro da jihar take ciki yas a suka zaɓi su yi taron a jihar Kano, domin tattauna hanyoyin ƙara magance matsalolin harkar Fawa, tsaftace harkar da kuma ƙara samar da haɗin kai.

A nasa ɓangaren mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, godewa ƙungiyar ya yi tare da karfafa musu gwiwa wajen gaba da sana’arsu bisa gaskiya da riƙon amana.

Taron dai ya gudana a rufaffen ɗakin taro na Zeenor Hotel da ke kan titin zuwa Gwarzo a birnin Kano.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan