A yau Lahadi aka ƙaddamar da sabon shugabancin tsagin tafiyar R – WIN WIN da ke cikin jam’iyyar APC reshen jihar Kano. Sanarwar ƙaddamar da sabon shugabacin na R – WIN WIN mai jerin shugabancin mutum 8 ƙarƙashin Malam Auwal Dankano da kuma shugaban kwamitin dattawan Malam Salisu Mangari, na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da su ka aikewa da manema labarai a birnin Kano.
Sanarwar ta ce bayan tuntuɓa tare da shawarwari akan tsarin tafiyar siysar WIN WIN a ƙarshe sun cimma matsaya kan kafa sabuwar ƙungiyar mai laƙabin R – WIN WIN tare da shugabanci da zai jagoranci tafiyar.

Jerin sababbin shugabannin da za su jagoranci tafiyar R- WIN WIN sun haɗa da Salisu Mangari a matsayin shugaban dattawa da Malam Auwal Dankano a matsayin shugaba da Buhari Ibrahim a matsayin Sakataren ƙungiya.
Sauran sun haɗa da Al- Mustapha Rano a matsayin Sakataren Kuɗi da Al – Mustapha Dankaro a matsayin Sakataren yaɗa labarai na 1 da Sani Mu’azu a matsayin jami’in hulɗa da jama’a na 2, da Usman Nur a matsayin daraktan walwala. Sauran su ne Aminu Gwarzo a matsayin sakataren tsare – tsare da kuma Sadiya Magashi a matsayin shugabar mata.

Hakazalika sanarwar ta ce sabon shugabancin na R – WIN WIN zai yi aiki kafada da kafada da dukkanin masu ruwa da tsaki da ke cikin gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma ƙunshin shugabancin jam’iyyar APC reshen jihar Kano da ke ƙarshin shugaban riƙon jam’iyyar Abdullahi Abbas da kuma kwamishinan ƙananan hukumomi Murtala Sule Garo, domin ƙara karsashin jam’iyyar.
Haka kuma sanarwar ta nemi yafiyar mai ɗakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje akan irin kalaman da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji ya yi akan ta a kwanakin baya.
Rundunar WIN WIN dai wani ɓangare ne a jam’iyyar APC da Injiniya Muaz Magaji ya ke jagorantar da nufin yin takarar gwamnan Kano a shekarar 2023 domin samar da sabuwar jihar Kano.
Sai dai tuni tafiyar ta WIN WIN ta haɗu da cikawa bayan da ɗaya daga fitattun masu ruwa da tsaki a tsarin tafiyar, Malam Auwal Dankano da ɗimbin magoya bayansa su ka ɓalle daga tafiyar WIN WIN ɗin tare da kafa sabuwa mai take R- WIN – WIN
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp