Badaƙalar Filaye: Hukumar EFCC na shirye-shiryen cafke Dakta Hafsat Ganduje

1335
farfesa Hafsat ganduje Goggo

Mai ɗakin gwamnan jihar Kano Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ki amsa gayyatar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar nan ta’annati – EFCC, ta yi mata a makon jiya da ɗan ta Abdulazeez ya kai korafi gaban hukumar kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Tun da farko hukumar ta EFCC ta gayyaci Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ne a ranar Alhamis ɗin makon jiya zuwa ofishinta da ke birnin tarayya Abuja.

Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje

Wata majiya ta bayyana cewa Abdulazeez wanda ɗa ne ga Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ya kai korafin mahaifiyar ta sa gaban hukumar EFCC ne bayan da wani mai sana’ar filaye da gidaje ya buƙaci ya yi masa hanyar wasu filaye a birnin Kano, wanda darajarsu ta kai ɗaruruwan dalolin Amurka tare da alkawarin inda aka dace zai samu kamashon Naira miliyan Talatin da Biyar.

Haka kuma majiyar ta ƙara da cewa wattani uku da Abdulazeez ɗin ya biya mahaifiyar ta sa ɗaruruwan dalolin, sai ya fahimci filayen da su ke buƙata an sayarwa da wani daban. Inda daga nan ne mai kuɗin ya buƙaci da a dawo masa da kudinsa.

Da aka tuntubi kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba akan batun ya ce ba shi da masaniya akan lamarin daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba. Haka shi ma kkakakin Hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwujaren bai ce komai akan batun ba.

Sai dai wata majiya daga hukumar ta EFCC ta tabbatar da cewa jami’an hukumar za su kama Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje inda har ta ki mutunta gayyatar, la’akari da cewa ita ba ta da wata rigar kariya da tsarin mulkin Najeriya ya ba ta.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

  1. […] Wani al’amari mai daukar hankali da kama da almara wanda yake fitowa daga jihar ta Kano kuwa, shi ne labarin da jaridun kasar nan ciki harda wannan jarida suka wallafa wanda yake nuni da cewa daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan jihar Kano wato Abdulazeez Ganduje ya maka mahaifiyarsa, Hajiya Hafsat Ganduje wacce aka fi sani da Goggo a gaban Hukumar Cin Hanci Da Rashawa wato EFFC kan zargin cin amana da karya yarjejjeniya. Ku Karanta: Badaƙalar Filaye: Hukumar EFCC na shirye-shiryen cafke Dakta Hafsat Ganduje […]

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan