Darajar Naira ta ƙara faɗuwa kan dalar Amurka warwas

421

Darajar Naira ta kai wani sabon mataki na faɗuwa inda ake canza dala ɗaya kan naira 549 a kasuwar bayan fage a ranar Litinin.

Yan kasuwa sun ce ana fama da ƙarancin dalar Amurka a kasuwa.

Naira ta kai matakin ne sakamakon matakan da babban bankin Najeriya ya ɗauka kan kasuwar masu canji a ƙasar nan.

A ranar Juma’a an sayar da dala ɗaya kan naira 545, a ranar litinin kuma ta kai naira 549.

Ana kuma sayar da dala ne kan naira 412 a farashin gwamnati a ranar Litinin.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan