Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da wa’adin kwanaki uku ga mazauna unguwar Hayin Ɗan Mani da su tattara su bar yankin a cikin kwanaki 21 ko kuma mazauna unguwar su biya jami’an hukumar KASUPDA kuɗin aikin rushe gidajensu.
Sanarwar da hukumar tsara birane da ci gaba ta jihar Kaduna wato KASUPDA, wacce babban daraktan hukumar Isma’il Umar Dikko ya sanya wa hannu tare da rabawa mazauna unguwar Hayin Da Mani, ta buƙaci da su kwashe tarkacensu da ke unguwar nan da kwanaki 21 idan ba haka ba gwamnatin za ta zo ta rusa gidajen da ke Unguwar kuma su biya ma’aikatan hukumar ladan rusawa.

Haka kuma sanarwar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon cin iyakar filin gwwmnati da mazauna unguwar su ka yi wanda hakan ya saɓa da doka.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na bayyana cewa wa’adin da ake debarwa mutane a kan su tashi daga gidajesu ba dai dai ba ne musamman idan anyi la’akari da halin da kasar nan ta ke ciki.
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin gwanna Nasiru El-rufai na cewa gwamnatin sa ta na aiwatar da aikin rushe gidaje da sauran wurare da aka gina ba bisa ka’ida ba a filaye mallakar gwamnati.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp