Muhammad Abdullahi Umar Ganduje ya kammala jami’ar Regent da ke birnin London

811

Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin yaye ɗaliban jami’ar Regent da ke birnin London a ƙasar Ingila.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa a birnin London

Cikin ɗaliban da su ka kammala wannan jami’a akwai Muhammad Abdullahi Umar Ganduje. Haka kuma Gwamna Ganduje na tare da mai dakinsa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran ƴan tawagar gwamnan sun haɗa da Kabiru Alhassan Rurum da Baffa Babba Danagundi da kuma Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan