Tayani Mu Gyara: Ƙalubalen da ke cikin aikin jarida a Najeriya (I)

575

Wanene Ɗan Jarida?

Ɗan jarida shi ne mai samo labarai yana yaɗawa a gidajen talabijin da jaridu. Ana samun Ɗan jarida mai zaman kansa ko kuma wanda zai rinka yiwa wata kafar yaɗa labarai, kamar Rediyo ko Talabijin. Akwai ire-iren Ƴan jaridu kamar, Mai rahoto (wanda yake bincike kuma ya rubuta sannan ya kawo rahoto.) Ƴan jaridu suna rubuta labarai da sharhi ga kafafen yaɗa labarai.

Haka kuma su kan yi bincike ne da hira da mutane da tambayoyi wajen rubuta labarai da rahotannin su. Dole ne masu rubuta labarai da sharhi su zama masu fadar gaskiya, domin fadar gaskiya yana da matuƙar muhimmancin gaske ga aikin jarida. Idan Ɗan jarida ya zama baya faɗin gaskiya a labaran sa ko kuma rahotannin sa to yakan fuskanci hukunci na dakatarwa ko ma kora baki ɗaya daga kafar yaɗa labaran da ya ke yiwa aiki.

A ɓangaren masana kuma malaman koyar da aikin jarida sun yi bayanin akan wanene ɗan jarida. Malam Salisu Uba Kofar Wambai da ke karatun digirin digirgir akan harkokin aikin jarida da kuma sadarwa a jami’ar da Bayero da ke Kano, ya bayyana ɗan jarida da cewa;

“Duk wanda ya yi karatun aikin jarida to wannan za a ce ya sami horon aikin jarida ne. Shiga kuma yin aikin jaridar wani abu ne mai zaman kansa. Da yawa akan samu bambanci daga abinda aka karanta da kuma wanda aka samu a aikin na zahiri. Dole mutum ya haɗa biyu wato ya samu horo sannan kuma ya yi aikin to daga nan ne za a kira shi ɗan jarida”

Wasu Ƴan Jarida A Bakin Aiki

Ya ƙara da cewa “Wanda bai karanta aikin jarida ba kuma ya samu kansa a cikin aikin jarida shi ma ba za a kira shi dan jarida ba kai tsaye ba. Sai dai a kira shi da Auxiliary journalist wato mai taimakawa ƴan jarida a aikinsu. Amma idan aka tura shi ya samu horo ko da na ƴan satittika ne, ya koyi basic aikin to ya zama ɗan jarida”

“Matuƙar mutum bai da horon to ba ɗan jarida ba ne. Shi ya sa zaka ga ana samun Political reporter, Economic reporter, Social reporter. Misali Economic reporter ya karanta Economic to sai kuma ya yi kwas (Course) a kan aikin jarida (Journalism) to ya zama ɗan jarida mai kula da ɓangaren tattalin arziki (Economic Desk) a gidan jarida. Wannan ita ce hanyar da aka bi a ka samar da ƴan jarida daga kowanne sashe na rayuwa. Ta haka ake samun masu rahoto akan kimiyya wato Science Reporters”

Ƙalubalen Da Ƴan Jaridu Ke Fuskanta A Najeriya

A wurare da dama dai, manema labarai ko ƴan jarida na fama da matsaloli yayin gudanar da aiyukansu, hatta a wasu ƙasashen da suka ci gaba, manema labaru ba su tsira daga irin waɗannan kalubale ba.

Sai dai a Najeriya rashin albashi mai kyau, da rashin cikakkiyar kula da walwala, da kare hakkokin ƴan jarida a Najeriya na daga cikin manyan ƙalubalen da ma’aikatan aikin jarida da yada labarai ke fuskanta.

Haka kuma cin zarafi da kai hari kan ƴan jaridu don sun gudanar da aikinsu na zama daya daga cikin babban kalubalen da ke fuskantar aikin jarida a Najeriya, wanda ake ganin karuwarsa a sassa daban–daban na ƙasar nan inda daga faɗar gaskiya ko kuwa bankado zargi na aikata ba dai dai ba, ake kai musu hari, baya ga barazana ko kokarin rufe musu baki.

Sai dai wani ɗan jarida kuma Editan jaridar Nigerian Tracker mai suna, Malam Abbas Yusha’u Yusuf, ya ce ɗaya daga cikin matsalar da ƴan jarida suke fuskanta shi ne rashin biyan su isasshen albashi, wanda hakan yana daga cikin matsalolin da su ke ragewa yan jaridar ƙwarin gwiwar fadin gaskiya komai ɗacin ta.

Sannan ya kara da cewa rashin isassun kayan aiki na zamani da kuma batun horar da su na cikin matsalolin da suke fuskanta, duba da yadda a kullum abubuwa ke canjawa a aikin jarida.

Duk da cewa masu ruwa da tsaki a bangaren kamar majalisar kula da ayyukan ƴan jarida ta ƙasa, da ƙungiyar editoci, da kuma ƙungiyar ƴan jarida ta NUJ, har ma da masu sharhi da rajin ci gaban aikin jarida a Najeriya sun dade suna gwagwarmayar wayar da kan hukumomi game da muhimmancin samar da tsarin da ya dace ga ƴan jarida, amma har yanzu a iya cewa kwalliyya ba ta kai ga biyan kudin sabulu ba.

Zamu Cigaba

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan