An yaba da ƙoƙarin da fitaccen mai taimakawa al’umma kuma mashahurin Farfesan nan da ya kafa jami’ar Maryam Abacha da ke da matsuguni a jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma rassa a birnin Kano da ƙaramar hukumar Gwarzo, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, na ganin ɗalibai a arewacin Najeriya sun mayar da hankali wajen koyon harshen Faransanci domin ƙarfafa dangataka tsakanin ƙasashen da ke makoftaka da Najeriya da su ke amfani da harshen.
Yabon ya fito ne daga bakin Farfesa Bashir Mohammed Sambo na sashen koyar da harshen Faransanci a jami’ar Bayero da ke Kano a lokacin da ya ke wata hira ta musamman da jaridar Politics Digest a ofishinsa.

Farfesa Bashir Mohammed Sambo, wanda shi ne Bahaushe na farko da ya zama Farfesa a harshen Faransanci ya ce ko a ƴan kwanakin nan sai da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ɗauki nauyin karatun dalibai guda 50 da za su karanta harshen Faransanci a jami’ar ta Bayero.
Haka kuma shehin Malamin ya ce ɗaukar nauyin karatun dalibai zai fara ne tun daga aji ɗaya na jami’a wato (Level 100) har zuwa kammalawa.
Hakazalika Farfesa Bashir Mohammed Sambo ya ce yadda Adamu Abubakar Gwarzo ke ɗawainiya da kuma ƙoƙari wajen bunƙasa harkar ilimi a jihar Kano da ma arewacin Najeriya abin a yaba ne. A dan haka ya buƙaci masu hannu da shuni da su yi koyi da shi.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo dai shi ne shugaban jami’ar Maryam Abacha da ke jamhuriyar Nijar, kuma gidauniyarsa ta shahara wajen taimakawa ilimi da kuma baiwa ɗalibai tallafin karatu tare da ɗaukar nauyin su.