Duk mai son kwanciyar hankali ya auri mace fiye da ɗaya – Naziru Sarkin Waka

1220

Fitaccen mawaƙi a masana’antar Kanywood Naziru M. Ahmed wanda aka fi sani da sarkin Waka ya yi kira ga magaidanta da su ke son kwanciyar hankali da ya auri mace fiye da ɗaya.

Naziru Sarkin Waka ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram a jiya Talata inda masu bibiyar sa su ka bayyana ra’ayin su tare da muhawara akan batun.


“In kana son kwanciyar hankali to matarka ta fi ɗaya”

Naziru Sarkin Waka ya ƙara da cewa “Me mata ɗaya … Allah ka aurar da mai son aure ko da kari zai yi”

Zama da mace fiye da ɗaya ta fuskar addini akwai umarni, umarni na wajibi da umarni wanda yake bana wajibi ba. Haka kuma adalci shi ne ginshikin aure ga duk ma’aurata ko da kuwa mutum ya auri mace ɗaya ko huɗu, adalcin kuma bai tsaya kan mace kaɗai ba ya shafi ƴaƴa da zuriya baki ɗaya, domin ubangiji yana gargadin tabbatar da adalci.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan