Asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Dawanau da ke jihar Kano ya bayyana cewa Abduljabbar Kabara ba shi da matsalar kwakwalwa.
A ci gaba da zaman sauraren ƙarar malamin da ake yi, duka lauyoyin Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis.
Wakilin BBC da ya halarci zaman kotun ya ce lauyan Abduljabbar daya ne ya je kotun Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar malamin.
Ya kuma ce “Sauran lauyoyin su ma sun janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu babu wanda ya halarci zaman kotun.
An ɗage sauraron ƙarar malamin zuwa 2 ga Satumba
A bayanin sakamakon gwajin asibitocin da aka gabatar wa kotun, Asibitin Dawanau na masu matsalar kwakwalwa ya ce an taɓa kwantar da Abduljabbar a asibitin na tsawon kwana hudu a baya.
“Lokacin da ya taɓa yin rikici da ‘yan uwansa an taɓa kwantar da shi a asibitin na kwana hudu, amma ba a taɓa yi masa gwaji ba kuma ba a taɓa ba shi magani ba,” in ji mai karanto bayani a gaban kotun.
Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda ke yin shari’ar, ya tambayi sakamakon Asibitin Murtala da aka kai Abduljabbar domin yi masa gwajin kunne, saboda gaza amsa tambayoyin da aka yi masa a zaman kotun na baya, wanda ake tsammanin ko ya samu matsalar kunne ne.
“A sakamakon gwajin kunnen da muka samu daga Asibitin Murtala, an tabbatar da cewa Abduljabbar ba shi da matsalar kunne ko kuma ji ko kaɗan,” mai gabatar da bayani ya ce.
Alƙali Yola ya ce ya amince da buƙatar lauyoyin Abduljabbar na janye wa daga kare malamin.
An ɗage sauraren ƙarar Malamin zuwa ranar 30 ga watan Satumbar 2021.
-
CITAD ta gano wani ƙauye a Kano da ke cikin gagarumar matsalar rayuwa
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato Centre for Information Technology and Development (CITAD), ta gano wani kauye a yankin ƙaramar Albasu a jihar Kano da al’ummar wannan kauye su ke fuskantar matsaloli daban-daban. Cibiyar ta CITAD ta rawaito cewa mutanen ƙauyen Yarimari – Hungu da ke cikin ƙaramar hukumar Albasu ta jihar Kano […]
Matashiya
A ranar 2 ga watan Satumbar da muke ciki ne wata Kotun Musuluncin da ke shari’ar Malamin ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da kunne a wani zaman ci gaban shari’ar da aka yi.
Kotu ta bayar da umarnin ne bayan malamin addinin Musuluncin ya gaza amsa tambayoyin da alkalin kotun Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa ranar 2 ga watan.
Lauyoyin da ke kare Abduljabbar karkashin jagorancin Barista Sale Bakaro sun soki yadda ake tsawaita shari’ar da kuma sabbin tuhume-tuhumen da aka gabatar kan Malamin.
Sai dai Alkali Sarki Ibrahim Yola ya ce a fahimtarsa wadannan tuhume-tuhume da aka gabatar wajibi ne domin a karanta wa wanda ake zargi laifukan da ake bukatar amsa daga gare shi.
Rahoton BBC Hausa
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp