Zamu baiwa Goodluck Jonathan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023 – Jam’iyyar APC

1876

Jama’iyya mai mulkin Najeriya APC ta bayyana cewa za ta bar tsohon shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya yi takarar shugabancin kasa karkashinta a kakar zaɓen shekarar 2023 idan ya dawo jama’iyyar.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Ssakataren kwamatin riko na jam’iyyar, John Akpanudoedehe a lokacin da ya ke tattaunawa da gidan Talabijin na Channels.

Tun bayan amsar mulki daga hannun Goodluck Jonathan, ba a taba jin wata mummunar kalma ta fito daga bakin Shugaba Buhari kan Jonathan din ba duk da cewa gwamnatin Buhari ta sha nuna wa tsohuwar gwamnatin yatsa kan wasu tuhume-tuhume.

Shugaba Muhammadu Buhari da Tsohon shugaban ƙasa Jonathan

Sai dai a wasu lokutan baya, Shugaba Jonathan ya sha yin hannunka mai sanda ga gwamnatin Buhari duk da cewa shi ma bai taba kama suna ba.

Haka kuma tuni manyan ƴan jam’iyyar ta APC da ake kyautata zaton za su tsaya takara a zaɓen shekarar 2023 suka fara wasa wuƙarsu, yayin da ya rage kusan shekaru uku a gudanar da zaɓen.

Masana na ganin cewa za a sha gwa-gwa-gwa wajen neman tikitikin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, la’akari da cewa akwai wasu manya da suka dafawa shugaba Muhammadu Buhari duk da suna da sha’awar shugabancin, amma a yanzu ana neman watsa musu ƙasa a ido.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan