An buƙaci Gwamna Ganduje da ya sallami Muaz Magaji daga mukaminsa

638

Shugaban ƙungiyar R WIN – WIN da ke cikin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Malam Auwal Dankano ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta sallamar shugaban kwamitin aikin shimfida bututun iskar gas da zai taso daga Ajakuta ya bi ta Kaduna sannan ya dangana da Kano wanda aka yi masa lakabi da AKK, Injiniya Muaz Magaji daga kan wannan shugabanci.

Malam Auwal Dankano ya bayyana hakan ne yau a Kano jim kaɗan da kammala karɓar rahoton da shugaban R – WIN WIN ya kafa akan yadda Mu’az Magajin ke yiwa jam’iyyar APC zangon ƙasa a matakin jiha da ƙasa tare da ƙafar ungulu da kuma raina shugabannin jam’iyyar.

Haka kuma Auwal Dankano ya ce rahoton kwamitin da ke ƙarƙashin Ssakataren kungiyar ta R – WIN WIN Malam Buhari Ibrahim Adamu ya bayar da shawarar sallamar Injiniya Muaz Magajin daga jam’iyyar APC.

“Mun yi kwamitin karkashin Sakataren R – WIN WIN Malam Buhari Ibrahim Adamu, inda rahoton kwamitin ya bayyana cewa Injiniya Muaz Magajin ba ya girmama shugabancin jam’iyyar APC, a dan haka mu ke kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya yi gaggawar cire shi daga muƙamin da ya ba shi”

A lokacin haɗa wannan rahoton wakilin jaridar Nigerian Tracker ya tuntubi Injiniya Muaz Magajin domin jin ta bakinsa a kan wannan batu sai dai bai daga kiran wayar da aka yi masa ba.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan