Masana a Najeriya sun ce abin fargaba ne ganin yada makamaia ke sake ƙaruwa a hannun ƴan bindiga a Najeriya
Wani sabon rahoto da aka fitar a Najeriya kan batun tsaro ya nuna an samun raguwar mace-mace da hare-hare a sassan kasar, sai dai kuma rahoton ya yi bayani kan yaduwar matsalar tsaro a wasu sassan ƙasar.
Rahoton wanda kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya gudanar ya yi bayani dalla-dalla kan matsayin kasar a yanzu da kuma irin nakasu da ci gaban da ake samu a yakar matsalolin tsaro.
Rahoton ya nuna yadda suka gudanar da nazari da bincike da tattara alkalumansu daga watan Janairu zuwa Agusta.
Sai dai Rahaton ya nuna cewa a cikin wadanan watanni, a watan Yuni aka samu alkaluma mai yawa na mace-macen a fadin Najeriya.
Shugaban kamfanin Dr Kabiru Adamu, a tattaunawarsa da BBC ya shaida cewa a watan Yuni mutum 1032 aka hallaka, sannan a watan Agusta nazarinsu ya nuna cewa an samu mutum sama da 612 a jihohi 29 na fadin Najeriya da aka hallaka.
Dr Kabir ya ce bambancin alkaluma tsakanin watan Yuni da Agusta ke nuna ragin da aka samu na wadanda ake hallaka.
Ayyukan ‘yan bindiga da masu satar mutane don kudin fansa ya daidaita yankuna da dama a arewa maso gabashin Najeriya
Rahoton ya bayyana cewa yankunan arewa maso yammaci da Arewa maso tsakiya da Kudu maso yammaci da Kudu maso gabashi su suka fi shiga barazana.
Sannan ya yi bayani kan yada barazanar kai hare-hare a arewacin Najeriya ya karu duk da matakan da gwamnatin tarayya ke dauka da jihohi.
Binciken ya kuma shaida cewa kashi 76 cikin 100 na sace-sace dalibai ya faru ne a shekara ta 2021, sannan kashi 48 cikin 100 na mutanen da aka sace ya faru ne a wannan shekarar ta 2021.
Kuma kashi 80 cikin 100 na sace-sace da mace-mace an aikatasu ne a arewacin Najeriya.
Akwai jihohin arewacin Najeriya 7 da suka rufe makarantunsu saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga a 2021.
Kan me binciken ya ta’allaƙa?
Dokta Kabir ya ce bincikensu ya ta’allaƙa akan alkaluman da suka tattara daga dukkanin kananan hukumomi na kasa 744 na jihohi 36.
Kuma suna tattara wannan alkaluman ne bisa abubuwa biyar da suka shafi ɓangarorin tsaro, kama daga aikata laifuka da hari da makamai da cin zarafin mata.
Binciken ya kuma nuna yadda rabuwar kai tsakanin gwamnatocin jihohi da tarayya ke taka rawa wajen sake ta’azara matsalolin tsaro, rikicin manoma da makiyaya.
Ya bada misali da kokarin tabbatuwar kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan hanyoyin kiwo, to sai dai an samu jihohin kudu 17 da suka fito da kudirin hana kiwon.
Ya ce wanann ya nuna cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka za a samu matsaloli da saɓani kan abin da kundin tsarin kasa ya tanada.
Dokta Kabiru ya ce wannan dalili ya sa suka fito da shawarwari biyu; kawar da matsalar nuna banbamci da danne hakki wanda ke nuna cewa barin abin a haka zai shafi tsaron kasa.
Harajin VAT
Ya ce abubuwan da ke ta’azzara tsaro a yanzu shi ne batun tattalin arziki da zamantakewa.
Don haka idan aka wayi gari aka amince jihohi suke tattara kudaden harajinsu na VAT, to akwai matsala saboda jihohin da basa samun wasu kudaden kirki za su shiga wahala.
“Idan gwamnatin tarayya ta daina samun kaso da take samu daga jihohi, hakan zai shafi abubuwan da take taimakon jihohi marasa karfi.”
Dokta Kabir ya ce rashin samun kudaden zai sake ta’azzara matsalolin tsaro da jefa jihohi cikin wani yanayi.
BBC Hausa
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp