Ƴan Najeriya na bayyana ra’ayin su akan liyafar da Pantami ya shiryawa Femi Fani Kayode

403

Ƴan Najeriya musamman ƴan Arewacin ƙasar na cigaba da bayyana ra’ayin su akan yadda ministan harkokin sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami ya gayyaci sabon kamun jam’iyyarsu ta APC, tsohon minista Femi Fani Kayode zuwa gidansa tare da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle liyafar cin abinci.

Tun da farko ƴan Najeriya na tsaka mamakin sauya sheƙar da Femi Fani-Kayode ɗin ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki, sai ga shi kuma katsam ministan sadarwa Isa Ali Pantami ya gayyaci Femi ɗin zuwa gidansa.

Shafin jaridar Labarai24 ya tattaro wasu daga cikin irin abubuwa da al’umma ke cewa akan wannan gayyata da Sheikh Isa Ali Pantami ya yiwa Femi Fani Kayode:

Malam Aisar Musa Fagge malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha da ke jihar Kano cewa ya yi “Gaskiya har ga Allah raina yayi matuƙar ɓaci ganin hotunan Sheikh Isa Aliyu Pantami da gawurtaccen Maƙiyin addinin Musulunci, maƙiyin Hausa-Fulani, maƙiyin Arewacin ƙasar nan, wato Femi Fani-Kayode. Na yi iya ƙoƙarin na haɗiye baƙincikin nan amma na kasa. Na san cewa ita wannan ƙazamar siyasar tamu dole larura za ta haɗa rago, doki, jaki, da alade zama waje ɗaya. To amma na kasa gane wannan hikimar ta tarbar ƙazami, la’ananne irin FFK a gidan malam tare da wannan fara’ar da wangale masa baki. Da a taro suka haɗu kamar haɗuwarsu a ɗaurin Auren Yusuf Buhari sam ba zan damu ba. Amma ace wannan baƙin arnen ya ce zai zo gidanka kuma ka tarbe shi da wannan fuskar? Haba don Allah”

Ko FFK kafirin amana ne? Ko kuma ina jin ita wannan dariyar ta “Illa an tattaƙu minhum tuƙa” ce? Muna kyautatawa malamai zato a abubuwa da yawa, kuma muna ba su kariya daidai gwargwado a duk lokacin da muka ga wasu za su ci mutuncinsu ba bisa haƙƙi ba. Acikin malaman Sheikh Pantami ya fi kowa samun tagomashin kariyar mabiya amma har ga Allah na kasa gane hikimar wannan tarba da ya yiwa mutumin da ban tsammanin a tarihin y’an siyasar ƙasar nan akwai wanda ya kai shi cin mutuncin addinin Musulunci da Musulmai. A haƙiƙanin gaskiya muna gab da shiga lokacin da almajirai za su fi malamai ta-ka-tsan-tsan, kishin addini da kuma aiki da addinin a aikace”

Sheikh Isa Ali Pantami da Femi Fani Kayode

Allah ya dawowa da malamanmu izzarsu da kwarjinsu da kamalarsu da kamewarsu, ameen

A ra’ayin Shehu Liman Abu Adirrahman cewa ya yi “A addinance Femi Fani Kayode maƙiyin musulunci da musulmai ne, a siyasance maƙiyin Buhari ne da APC, a ɓangarance maƙiyin Arewa da ‘Yan Arewa ne, a ƙabilance maƙiyin Hausa Fulani ne, ƙiyayya ta zahiri ba ta baɗini ba”

Muna fatan Allah Ya sa Malam Pantami taƙiyya yake masa, domin mun san ba zai ɓoyu gare shi cewa FFK maƙiyin komai ne da shi Malam ɗin ke dangantuwa zuwa gare shi. Muminai bai kamata a yaudare shi ba kuma shima bai yaudara, bisa kyautata zato malam na amfani ne da ayar kan FFK ɗin”

ka tunkuɗe mummunan da aka maka da abu mafi kyau, ina ka yi haka sai wanda ƙiyayya ke tsakaninku ya zamo tamkar masoyi majiɓinci, ba wanda ake sanyawa irin wannan hali sai waɗanda suka yi haƙuri, ba waɗanda ake sa wa irin wannan hali sai masu babban rabo. “

Bello Matawalle da Isa Ali Pantami da kuma Femi Fani Kayode

Shi ma Bashir Uba Ibrahim cewa ya yi “Yanzu dai kalar Hon. Pantami ta gama fitowa. Mun gano kukan da yake yi a baya a she na neman mulki ne. Da Jonathan zai koma APC Pantami ne na farko a wadanda za su fara wanke shi duk da a baya ba irin aibata shin da be yi ba. Allah ya kyauta”

Amma a ra’ayin Abdulmumin Usman cewa ya yi “Ai Hon Sheik Isa Ali Pantami akwai dubara, ga shi ya iya kira (da’awa) cikin hikima da kyakkyawar mu’amala, shi yasa ya kawo shi har gida ne. Ƙila ma musuluntar da shi zai yi”

Shi ma Wada Nas cewa ya yi “Isah Pantami ai Ɗan siyasa ne yanzu Yakamata talakawa sugane da masu ɗaure masa gindi. Duk wani zagi da za’ayi wa Yan siyasa idan anmasa kada ranku ya ɓaci”

A ra’ayin Salisu Yahaya Hotoro kuwa cewa ya yi “Bari dai na cire tsoro nayi abin da ya dace!!!

“Gaskiya Hon. Isah Pantami bai kyauta ba a matsayin sa na musulmi Ɗan Arewa ya girmama Ɗan Tasha irin FFK, mutumin da bashi da aiki sai zagin mutanen Arewa da addinin Islama

“Ta inda abin yafi ɓatamin rai ace mutum kamar Pantami da wasu ke yiwa kallon Malamin addinin Musulunci ya gayyato mutumin da ya kira Sheikh Usman Ɗanfodio a matsayin Ɗan ta’adda har ya zauna yana cin abinci suna wasa da dariya da shi.

Wannan lamari yayi muni, giyar mulki ai ba hauka ba ce”

Femi Fani-Kayode ya yi kaurin suna wajen tayar da kura a shafukan sada zumunta musamman a Twitter da kafafen yada labarai. Haka kuma ba wai ya tsaya kawai wajen caccakar gwamnatin APC da shugaba Buhari kadai ba ne, Fani-Kayode mutum ne mai yawan yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da Hausawa har ma da Musulmai.

Sai dai har kawo lokacin haɗa wannan rahoton minista Isa Ali Pantami bai ce komai akan batun ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan