Tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu ya samu damar hawa matsayin gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ke Arewacin Najeriya, a cikin wani shirin da ake ɗauka.

Shirin wasan mai suna The White Lion an shirya shi ne domin nuna irin gudunmawar da Gwamna Yahaya Bello ya samar ga al’ummar jihar sa.

Shirin wasan na The White Lion ya mayar da hankalin akan yadda Gwamna Yahaya Bello ya bayar da gudummawa ga matasan jihar Kogi da kuma ɓangaren harkokin siyasa.

Ali Nuhu dai ya kasance fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, inda ya taɓa yin ikirarin cewa wasu jaruman fina-finan na Hausa na da kudurin tsayawa takara a zaben kasar nan da ke tafe.
Turawa Abokai