Farfesa Isa Ali Pantami ya shiryawa Femi Fani Kayode liyafa ta musamman

436

Ministan harkokin Sadarwa Sheikh Isa Pantami ya shiryawa sabon dan jam’iyyar APC Chief Femi Fani-Kayode liyafar cin abinci a gidansa.

A cewar Mista Fani-Kayode, ministan ya gayyace shi, shi da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle.

“Ni da abokina kuma dan uwana Gwamna Bello Matawalle, mun ji dadin karamci and girmamawa da gayyatar liyafar cin abinci da abokina kuma dan uwana ministan Sadarwa Farfesa Isa Pantami ya gayyace mu a daren jiya, a gidansa na alfarma,” a cewar Mista Fani-Kayode a shafinsa na Facebook.

Gwamna Bello Matawalle da Isa Pantami da kuma Femi Fani Kayode

Ya ce sai da su ka raba dare su na hira kan al’amuran kasa da na waje.

Wanene Femi Fani Kayode?

Femi Fani-Kayode, dan kabilar Yarbawa ne daga kudu maso yammacin Najeriya kuma tsohon ministan sufurin jiragen saman kasar, wanda ya yi kaurin suna wajen tayar da kura a shafukan sada zumunta musamman a Twitter da kafafen yada labarai.

Kuma ba wai ya tsaya kawai wajen caccakar gwamnatin APC da shugaba Buhari kadai ba ne, Fani-Kayode mutum ne mai yawan yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da Hausawa har ma da Musulmai.

Tun lokacin da aka kaddamar da shari’ar Musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya, Fani-Kayode ya ci gaba da sukar lamirin gwamnatocin jihohin da suka kaddamar da ita, da hakan ya sa ya rasa tagomashi a idanun al’ummar yankin arewacin kasar.

Rayuwa da kuma karatun Femi Fani Kayode

An haifi Femi-Fani-Kayode a jihar Lagos, kudu maso yamamcin Najeriya a ranar 16 ga watan Oktobar shekarar 1960 daga kabilar Yarbawa.

Mahaifansa Chief Remilekun Adetokunbo Fani-Kayode da Chief (Mrs) Adia Adunni Fani-Kayode sun rada masa suna David Oluwafemi (ma’ana ” wanda Ubangiji yake so”) Adewunmi Fani-Kayode.

Femi Fani Kayode

Fani-Kayode ya fara karatunsa a Kwalejin Brighton da ke Birtaniya tun yana da shekara 8. Kana a shekarar 1980 ya fara karatu a Jami’ar London inda ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin shari’a a shekarar 1983.

kuma shiga Jami’ar Cambridge, inda kakansa, da mahaifinsa da kuma yayansa duka suka yi karatun lauya.

Bayan kammala karatunsa a jami’ar ta Cambridge ne ya dawo gida ya fara karatu a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya inda ya kammala a shekarar 1985.

Ya kuma yanke shawarar tafiya kasar Ghana don yin karatun tauhidi a makarantar koyon addinin Kirista a birnin Accra, inda ya samu takardar difiloma a fannin tauhidin a shekarar 1995.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan