Rabe – raben ‘Malaman Addinin Musulunci’ a Najeriya – Nasiru Salisu Zango

    830

    Fitaccen ɗan jaridar nan da ke gabatar shirin ‘Inda Ranka’ a gidan rediyon Freedom da ke birnin Kano ya bayyana rabe-raben Malaman addinin Musulunci a yankin Arewacin Najeriya.

    Nasiru Salisu ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi mai taken Kukan Kurciya a shafinsa na facebook a yau Asabar.
    Ga rubutun da Nasirun ya yi kamar haka:


    Malamai sun ka su kashi kashi akwai malaman Allah da ke wa’azi tsakani da Allah su waɗannan sun fi fifita lahira akan duniya. Akwai Malamai ƴan siyasa waɗanda wa’azin ma na siyasa su ke, yadda ƴan siyasa ke sauya sheƙa su ma haka su ke, waɗannan ba malaman Allah ba ne, duniya ce a gaban su, ba za ka ji sun yi wa’azi ba sai abin da ya yi daidai da muradin iyayen gidan su. Tare ake cin ganimar siyasa da su wani lokacin ma har babakere su ke akan dukiyar na ƙasa dasu har akai ga EFCC”

    Nasiru Zango ya ƙara da cewa “Malamai ne marasa tawali’u masu wawaso akan kuɗin hadaya na alhazai, irin waɗannan Malamai ba su fiye yin wa’azi dan Allah ba sai dan birge iyayen gidan su. Kaɗan daga siffofinsu ke nan mu ka wassafa”

    Nasiru Salisu Zango

    Ina jinjina ga Malamai na Allah masu wa’azi tsakani da Allah waɗanda ba duniya ce a gaban su ba. Su kuwa rukunin Malamai ba duniyai muna kallon ku, kuma duk abin da aka fada akan ku, ba a taɓa muhibbar Malamai ko malanta ba. Duniya ce a gaban ku kuma muma gamu a cikin ta. Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta

    Kalaman na Nasiru Salisu Zango na zuwa ne kwana ɗaya da wani faifan bidiyo ya karade shafukan sadarwa na zamani, inda a ciki Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ke bayanin cewa kaso saba’in (70) na fitintunan da su ke faruwa yan jarida ne ke haifar da su.

    Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

    Facebook
    YouTube
    Instagram
    Telegram
    Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

    Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan