Fitila: Sharhin Manyan Rahotonnin Makon Jiya

435
Jarida

A wannan makon zamu fara sharhi ne daga birnin Kano, inda zamu fara da labarin da ya dade yana ciwa mutanan jahar tuwo a kwarya, wato karar da gwamnatin jihar ta shigar tana zargin Abduljabar Sheik Nasiru Kabara akan cin zarafin fiyeyyen haliita, Annabi Muhammd (SAW), tun a baya kunji yadda muka kawo muku zaman kotu wadda akayi a watan da ya gabata, kuma kunji yadda mai shari’ar kotun musuluncin nan wato mai Shari’a Sarki Yola ya umarci da a aike da Malam Abduljabar asibitin mahaukata na Dawanau domin duba lafiyar kwakwalwarsa, sannan kuma a duba lafiyar kunnensa.

Ku Karanta: Fitila: Sukuwa Da Zamiyar Yan Jarida A Makon Jiya

Abduljabar Sheik Nasiru Kabara

Wannan dai ya faru ne bayan da alkalin kotun ya karantowa wanda ake zargin laifuffunkan da ake zarginsa amma malamim yayi gum yaki cewa komai. Sai dai bayan dawowarsu kotu a wannan makon lokitoci sun sanarwa da mai Shari’ar cewa malamin lafiya lau yake, babu abinda ke damunsa.

Jim kadan bayan sanarwar sai kuma lauyoyin wanda ake karar suka shaidawa mai shari’a cewa sun dakatar da kare wanda ake karar nan take.

Yan jarida masu son sanin abinda ya wanzu har ta kai ga lauyoyi suka janye kariyar da suke bawa malamin sun tuntubi jagoran lauyoyin domin bayar ba’asin abinda ya faro, sai dai lauyoyin sun shaidawa yan jaridar cewa ba za suce komai game da lamarin ba saboda dokakin aiki. Amma suna so malamin ya janye wasu zarge-zarge da yake musu idan ba haka ba zasu maka shi a kotu.

Sai dai wata majiya wacce ta fito daga malamin tana nuni da cewa Malamin ya raba gari da lauyoyin nasa ne sakamakon sanarwar da suka bashi a baya ta cewa yayi shiru kar yace komai in an karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, inda suka shaida masa cewa yin shirun nasa bashi da wani hukunci a shari’a, sai dai bayan aikata abinda lauyoyinsa suka umarta ke da wuya sai yaji mai shari’a yace a aike dashi asibiti, wadda wannan ne ya tunzura malamin kuma yake ganin kamar lauyoyin sunyi masa ingiza mai kanto ruwa, wato sun bashi gurguwar shawara. Wanda wannan ce ta sa ya raba gari da lauyoyin nasa.

To komai wannan yake nunawa? Wannan shafi na www.labarai24.com ya tuntubi masana harkokin shari’a da masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum domin jin yadda suke ganin wannan batu, inda suke ganin lallai akwai kuskure a wurin dukkanin bangarorin gudu biyu, a cewar wani babban lauya mai mukamin SAN, yana ganin cewa kamata yayi lauyoyin da wanda suke karewa su samarwa da kansu masalaha amma ba wannan tereren da suke yiwa juna ba.

Inda yace wannan ba zai haifarwa da kowanne bangare daga cikinsu da mai ido ba. Yau ma dai nan zamu ajiye wannan batu, za kuma muci gaba da bibiya.

Wani al’amari mai daukar hankali da kama da almara wanda yake fitowa daga jihar ta Kano kuwa, shi ne labarin da jaridun kasar nan ciki harda wannan jarida suka wallafa wanda yake nuni da cewa daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan jihar Kano wato Abdulazeez Ganduje ya maka mahaifiyarsa, Hajiya Hafsat Ganduje wacce aka fi sani da Goggo a gaban Hukumar Cin Hanci Da Rashawa wato EFFC kan zargin cin amana da karya yarjejjeniya. Ku Karanta: Badaƙalar Filaye: Hukumar EFCC na shirye-shiryen cafke Dakta Hafsat Ganduje

Kamar yadda jaridu suka rawaito, babban dalilin kai mahaifiyar tasa gaban EFFC shi ne game da wani cinikin fili wanda ake zargin shi Abdulazeez yayiwa wani attajiri jagora aka sayarwa ta hannun mahaifiyar tasa, inda shi kuma ya samu la’adar naira miliyan talatin, amma sai daga baya wanda ya sayi filin yaji an sake sayarwa da wani mutum daban filin.

farfesa Hafsat ganduje Goggo
Hajiya Hafsat Ganduje (Goggo)

Nan take attajirin ya nemi da a maida masa da kudinsa domin yana ganin baici nanun-ba-nanun ba zata ci shi ba. To amma dai rahotanni da suke fitowa daga EFFC sun nuna cewa kudaden sun gagara fitowa inda shi kuma Abdulazeez ya garzaya gaban EFFC domin nemo hakkin attajirin.

Har kawo yanzu ba’a samu jin ta bakin gwamnatin Kano ba, sannan ita ma hukumar EFFC taki cewa komai game da batun. Shima wannan batu nan zamu jingine shi, amma zamu cigaba da bibiya.

A bangaren tsaro kuma, wanda shi ne yafi daukar hankalin al’ummar kasar musamman mutanen dake yankin Arewa masu Gabas, an samu rahoton kai hari gidan kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru Mu’azu Magarya inda aka rawaito cewa yan bindiga sun kone gidan kakakin majalisar tare da wasu gidajen al’umma a garin Zurmi dake jihar Zamfara.

Yan Bindiga

Duk da dai ba’a samu labarin rasa rayuka ba, amma mai bawa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro da hukunta yan bindiga a jihar, Alhaji Abdullahi Shinkafi yace “kai harin baya rasa nasaba da nasarorin da sojoji suke samu akan yan bindiga bayan fito da wasu dabaru da dokoki da zasu taimaka wurin hana yan bindigar sukuni a jahar”.

Haka ma kuma a dai bangaren tsaron an samu labarin sace sarki mai daraja ta daya, Alhaji Hassan Attahiru, Sarkin Bundugu dake jihar Zamfara akan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Wannan hanya dai a kwanakin baya tayi kaurin suna wurin sace-sacen mutane wanda yan bindiga suke yi, amam dai a yan kwanakin nan an samu saukin sace-sacen in banda wannan da aka sami labarinsa a ranar Talatar da muka yi ban kwana da ita.

Wannan al’amari dai masana tsaro suna alakanta shi da cewa mai yiyuwa yan bindigar sun biyo basaraken ne daga inda ya taso kuma suka samu damar cin masa a wannan yanki. Harkokin tsaro dai kullum kara tababbarewa suke yi a wannan yanki, inda dubban al’umma suke rasa rayukansu wasu kuma ake mayar dasu yan gudun hijira ta karfi da yaji.

Masana da dama suna ganin akwai gazawar gwamnatoci kama daga na tarayya har zuwa na jahohi wurin yaki da yan ta’adda. Inda wasu suke zargin akwai sa hannu manya-manyan mutane a cikin wannan harka, kamar yadda gwamnan Zamfara ya fada a kwanakin baya da dai sauran masu fada aji a yankunan.

A wannan mako zamu rufe wannan shafi da maganar dake yamutsa hazo tsakanin wasu jahohi da gwamnatn tarayya akan kabar harajin yau da kullum wadda ake kira VAT.

Makon da ya gabata ne muka labarta muku cewa tuni jihar Lagos da Rives suka yi dokar karbar haraji a jahohinsu duk da dai kotun daukaka kara ta dakatar da su. Wasu sabbin al’amura da suke bullowa game da wannan batu sun hada da taron da gwamnonin yankin Gabas suka yi inda baki dayansu suka amince kan karbar harajin VAT a jahohi.

Sai abu biyu wanda shi ma yana da jibi da wannan batu, a ranar talatar da ta gabata ne majalisar dokokin jihar Kano ta umarci shugaban hukumar karbar haraji ta jihar da ya gurfana a gabanta, inda bayan wasu tambayoyi da titsiye, majalisar ta ba wa gwamnan jihar umarnin sauke shugaban hukumar cikin awa arba’in da hudu.

Haka kuma gwamnatin ta Kano ta fitar da sanarwar cewa tana dab da yin doka da zata fara karbar harajin yau da kullum a jihar kamar yadda jihar Lagos da Rivers suka yi.

Shin wannan zai haifarwa da kasar da mai ido?

Masana na ganin cewa karbar wannan haraji daga jahohi zai jefa kasar cikin rudani, domin za a ringa samu mabanbantan haraji, kuma harajin zasu yiwa kwanfanoni yawa wadda zai sa dole wasu kwanfanonin su rufe saboda da yawan haraji kamar yadda ta faro a Indiya a shekarun baya kafin su dawo harajin bai daya kamar yadda akeyi a Najeriya yanzu.

Sai kuma wasu bangarorin da suke ganin cewa yin hakan zai zaburar da wasu gwamnonin su samo hanyoyin samun kudi na cikin gida, sannan zai rage lalaci da cima zaune na da yawa daga cikin gwamnoni wadanda ba abinda suke sai jiran karshen wata a turo kudi daga gwamnatin tarayya su yi albashi su raba sauran.

Ali Sabo

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email –Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan