Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ƴan Jarida

  675

  Huɗubar da Da Sheikh Mallam Aminu Ibrahim Daurawa ya yi wadda ta tayar da jijiyoyin wuya, har ta sa wasu suke ganin an taɓa mutuncin sana’ar su, ba tare da sa ka kaifin hankali da nutsuwa wajen tantance gaskiyar maganganun shehin malamin ba, masu ƙarancin kunyar cikinsu suka fito suna yiwa malamin raddi, wasu kuma su ka yi shaguɓe amma masu ilimi da hankalin cikinsu nutsuwa suka yi suka dubi huɗubar malamin da idon basira suka tabbatar da akasarin maganganunsa haka su ke.

  Da yawa daga cikin ƴan jarida wannan mas’alar na yaɗa labarun ƙarya, ƙage da sharri ba tare da tantancewa ba tana damun su amma ba yadda za su yi. Allah ya ji ƙan Mallam umar Sa’idu Tudun Wada mun sha tattauna wannan matsalar da shi musamman lokacin da ya ke shugabancin rediyon Kano (MD Radio Kano), ya ke ce min babban burinsa shi ne kawo sauyi a gidan radiyon na hana labaran ƙarya, da amfani da gidan rediyon wajen cin mutuncin wani, ko da kuwa ta ɓangaren gwamnati ne.

  A kwanan nan wani wasan kwaikwayo ya bayyana yadda ƴan jarida su ke karɓar na goro, haka wasun su ka dinga habaice habaice wasu har da zage zage, na ce lalle Allah bawa sojoji haƙuri su da suka sadaukar da rayuwarsa wajen kare Al’umma amma da zarar sun yi wani da kuskure ko aka sami akasi sai al’umma su yi musu chaa, da maganganu marasa daɗi amma basu taɓa mayar da martani da makamin da ke hanunsu ba, kamar yadda ƴan jarida su ke amfani da nasu makaman. Misali baya – bayan shi ne na harin da aka kai makarantar horon sojoji da ke Kaduna wato NDA, amma sun manta an taɓa kai hari cibiyar tsaron ƙasar Amurka wato PENTAGON.

  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

  Haƙiƙa aikin jarida a baya – bayan nan ya sake taɓarɓarewa sakamakon yawaitar kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu da mainstream da social media.

  Wannan ɗabi’ar ta gurbattatun ƴan jarida ba wai aikin jaridar ba ne ya ke koyar da shi, a a halaiya ce kawai ta gurɓatattun cikinsu, hasali ma aikin jarida koyar da tsabtace aikin ya ke yi da inganta shi, yana da ƙa’idoji na tantance labari kafin ka yaɗa shi. Na san wannan lokacin da na yi karatu a jami’ar Bayero na yi subside da Mass Communication, to amma inda matsalar take sau tari wasu gidajen rediyon ba sa ɗaukar ƙwararru aiki da yawa wasu da takardar Sakandire ake ɗaukarsu musamman idan suna da zaƙin murya ko iya sarrafa zance, ko kuma in sun je sanin makamar aiki (Attachment) a riƙe su ko da kuwa ba fanin suka karanta ba. Wasu daga baya su kan je su ƙaro karatu ko kos ɗin sanin makamar aiki, amma akasari ba sa chanja halinsu saboda gani suke sai sun fi suna a halinsu na rashin daraja.

  Kamar yadda Mallam Aminu Daurawa ya faɗa malami zai yi shekaru yana aikata aikhari ba sa faɗa amma lokaci guda idan ya yi kuskure sai su yi caa akan sa har da ƙarin gishiri.

  Haƙiƙa aikin jarida aiki ne mai matuƙar amfani ga wacce irin al’umma, saboda muhinmancin sa a wasu ƙasashen sanya shi suke a na hudu a tsarin gudanarwar gwamnati, suna kiransa Fourth Estate of The Realms kamar su Executive, Legislature da Judiciary saboda muhimmancin aikin ga Al’umma.

  Amma dai Alhamdulillahi alkhairansu ya fi sharrinsu yawa wasu kalilan ne su ke bata musu suna.

  Allah ka sa su gyara ko don gano su da al’umma su ka yi saɓanin a baya duk abin da ɗan jarida ya faɗa gaskiya ne babu mai ƙalubalantar sa. Akulu haza astagafirillahu li wa lakum

  Aminu Hassan ya rubuto daga cikin Kano

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan