Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma kwamishinan ayyukan gona na jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya yi wata ganawa sirri da tsofaffin shugabannin Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdulsalam Abubakar a birnin Minna da ke jihar Neja.

Tun da farko shafin Instagram na Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ne ya wallafa labarin ziyarar a jiya Lahadi.

Tuni masu sharhi akan al’amuran da su ka shafi siyasar Kano ke ganin ziyarar na da alaƙa da neman goyon bayansu a zaɓen shekarar 2023.

Tuni dai uwar gidan Gwamnan Kano Hajiya Hafsatu Abdullahi Ganduje ta bayyana cewa Kwamishinan Kananan hukumomi Murtala Sule Garo shi ne zai gaji mai gidanta a zaben na 2023, wanda hakan ya rura wutar rikici a jam’iyyar musamman ganin akwai wasu makusantan Gwamna Ganduje da ke neman kujerar.