Raddi: Duk ɗaukakar da Sheikh Aminu Daurawa ya samu silar aikin jarida ce

  879

  RADDI: DUK DAUKAKAR DA MALAM DAURAWA YA SAMU TANA DA ALAKA DA SHIRIN KUNDIN TARIHI NA FREEDOM RADIO DA SHIRIN TAMBAYA MABUDIN ILIMI NA PYRAMID RADIO

  A zahirin gaskiya bamu da ilimi ko gogewar da zamu ja da masana irin su Malam Daurawa. Amma fi sabilillahi Malam yana daga cikin mutanen da basa yiwa bakin su linzami, musamman akan mas’alolin jama’a da zamantakewar al’umma.

  A ranar Juma’a 17 ga watan September 2021 ya yi wata khudubar juma’a, inda ya zargi yan jarida da abubuwa da dama. Cikin laifukan akwai cewa “duk rikicin dake faruwa a duniya da duk tashin hankalin dake faruwa a duniya ‘yan jarida ne suke haifar dashi, hatta a lokacin annabi (S.A.W)”.

  Malam ya kuma kama sunan wasu shirye shirye irin su INDA RANKA na Freedom Radio a cikin misalan sa. A gani na wannan cin mutunci ne ga hanyar neman abincin wasu mutane ciki har da ni. Kuma mashiryin Inda Ranka wato Nasiru Salisu Zango ya na bawa al’umma gudunmuwar da a ta wuce tunanin duk mai tunani wallahi. Duk da irin aibu na Malam musamman tsundumar shi sabgogin siyasa bamu taba fitowa mun haskawa duniya irin wadannan abubuwan ba saboda kara irin tamu ta yan jarida. Mu dubi Allah muyi adalchi.

  Allah ya bada hakuri na san zan fuskanci kakkausar suka daga almajiran Malam, nima masoyin Malam ne kuma mai masa fatan alkhairi.

  Gidado Sidi Mustapha (Guarantee Radio, Kano)

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan