Sarkin Zazzau Shehu Idris ya cika shekara guda da rasuwa

460

A yau Litinin 20 ga watan Satumbar shekarar 2021 marigayi mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris ya ke cika shekara ɗaya cif da rasuwa.

Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu ranar Lahadi 20 ga watan Satumbar shekarar 2020 bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

Haka kuma marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84, bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris


Tuni dai zuri’ar Katsinawa a masarautar Zazzau su ka shirya wata addu’a ta musamman domin neman rahamar Allah ga marigayin.

Hakazalika ƴan masarautar na cigaba da alhinin rashin Sarkin na su da su ke masa take da Balaraben Saraki.

Kasimu Hanwa wani makusancin ne ga Sarkin Bai Zazzau, Alhaji Ashiru Isa Kudan ya bayyana cewa “Yau satin ka Hamsin da Biyu (52) da rasuwar ka, muna Addu’a Allah ya gafarta maka da rahma Ameen”

Shi kuwa Ibrahim Abdullahi Abdul cewa ya yi “Baba Mai Martaba Alhaji Shehu idris Sarkin Zazzau Sarki na sha Takwas a kasar Zazzau. Muna maka addu’a Allah ubangiji yasa aljanna makoma Allah ubangiji ya cigaba da lillibika da rahamarsa a wannan rana da muki tunawa da kai da kuma yima addu’ar shekara daya da barinmu Allah ya yalwata kabarinka da rahma”

Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Manyan mutane wadanda suka hada da tsoffin shugabannin Najeriya, da gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin tarayya, da sarakuna da manyan jami’an gwamnati ne su ka ziyarci birnin Zazzau domin yin ta’aziyyar Marigayi Dokta Shehu Idris

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan