Labarin ƙauyen da al’ummar sa ke shan ruwa tare da karnuka a Kano

582

Ruwa aka ce shi ne ginshikin rayuwa, don haka samar da tsabtatatcen ruwan sha ga jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace gwamnati.

Haka kuma tarihi ya nuna cewa gabanin shekarar 1960, lokacin da Najeriya ta samu ƴancin kanta daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila, ƴan kasuwa ne ke tafiyar da harkar samar da ruwan sha da ma na amfanin jama’ar ƙasar nan.

Har sai a shekarar 1962 zuwa 1968 ne gwamnatin ta fara shiga harkar samar da ruwa, a lokacin da ta kafa hukumar raya kogin Naija da ta raya tafkin Chadi, waɗanda aka dorawa alhakin zana taswirar wuraren da ake samun ruwan da za a yi amfani da shi wajen noma, kamun kifi, kiwo da ma zirga-zirgar jama’a, sai kuma hukumomin samar da ruwan sha a manyan-manyan birane, inda aka yi watsi da yankunan karkara.

Yara a ƙauyen Nera da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a kan hanyarsu ta tafiya neman ruwa

Wannan ce ta sanya al’ummar ƙauyen Nera da ke yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano su ka auka cikin matsalar ƙarancin ruwan sha, inda su ka koma sha tare da amfanin yau da kullum da ruwan wani rafi da ke ƙauyen wanda shanu da awaki da kuma karnukan da ke zagaye da wannan ƙauyen su ma nan ne inda su ke shan wannan ruwa.

Tun da farko ɗaya daga cikin Editocin jaridar Nigerian Tracker da ke yaɗa labaranta a shafukan intanet, Misbahu El-Hamza ne ya wallafa hotunan tare da labarin yadda al’ummar wannan ƙauye ke fuskantar wannan matsala ta ruwan sha.

Al’ummar wannan ƙauye sun bayyana cewa ba su da wani zabi da ya wuce amfani da wannan ruwa domin ba su da wanda ya fi shi.

Wata yarinya mai suna Aya yar kimanin shekaru 16 da aka tarar da ita a wannan rafi ta zo diban ruwa ta bayyana cewa ba su da zaɓin da ya wuce amfani da wannan ruwa.

“Shi ne ruwan da mu ke sha kuma mu yi girki da shi da sauran ibada. Bamu da wani ruwa a wannan ƙauye da ya fi shi”

Ƙarancin tsabtataccen ruwan sha a jihar Kano na ci gaba da kasancewa wata babbar annoba birni da kauye, lamarin da ya sake dawo da harkar samar da ruwan sha ga hannun ‘yan kasuwa, da ke giggina rijiyoyin birtsatse suna saidawa jama’a ruwan da za su yi amfani dashi, wuraren da ba rijiyoyin birtsatsen kuma jama’a kan dogara ne kawai ga kowane irin ruwa suke da shi a wajen su koda kuwa ba tsabtatacce bane.

Wannan ne kuma ke kawo cutukan da ake samu ta ruwa kamar kwalara wato amai da gudawa.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan