Shugabancin APC A Kano: Ganduje na shirin canza Abdullahi Abbas da Mukhtar Ishaq Yakasai

5263

A dai-dai lokacin da ya rage ƙasa da makonni biyu a gudanar da zaɓen jam’iyyar APC a jihohin Najeriya 36, wata majiya a fadar gwamnatin Kano ta bayyanawa jaridar Labarai24 cewa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje na shirin canza shugaban riƙon jam’iyyar Abdullahi Abbas da kwamishinan ayyuka na musamman Mukhtar Ishaq Yakasai.

Majiyar da ta buƙaci mu sakaye sunanta ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ɗauki matakin goyon bayan Mukhtar Ishaq Yakasai ɗin ne sakamakon wasu dalilai da su ke nasaba da samar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar ta APC reshen jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

“Maganganu da kuma neman biyan kasuwar buƙata sun yi yawa a gaban mai girma Gwamna, domin shi mai riƙe da shugabancin jam’iyyar wato Abdullahi Abbas da kuma mai ba shi shawara na musamman akan harkokin abinci Alhaji Ahmadu Haruna Zago dukkanin su gwamna ya na ganin girmansu da darajarsu”

“Kuma kowanne a cikinsu ya matsa akan neman goyon bayan gwamnan akan wannan buƙata. Wannan ce ta sanya Gwamna Abdullahi Umar ya fito da Mukhtar Ishaq Yakasai domin raba rigima”

Jam’iyyar APC dai a jihar Kano na ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda ake alaƙantawa da zabukan shugabannin jam’iyyar da kuma son gadon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaɓen shekarar 2023.

Alhaji Mukhtar Ishaq Yakasai dai ya taɓa rike muƙamin shugabacin ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye, kuma a shekarar 2019 ya nemi jam’iyyar APC da ta tsayar da shi takarar majalisar tarayya sai dai ya yi rashin nasara a hannun Sha’aban Ibrahim Sharada.

Alhaji Mukhtar Ishaq Yakasai

Tuni dai jam’iyyar APC a matakin ƙasa ta sanar da ranar 2 ga watan Oktobar da ke tafe a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen Shugabancin jam’iyyar a matakin jihohi.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan