Kanywood: Na kamu da tsananin soyayyar Sheikh Isa Pantami – Hadiza Gabon

3450

Fittaciyar jarumar masana’antar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, ta bayyana yadda ta kamu da matsanaicin soyayyar Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.

Jarumar wadda mahaifiyarta ƴar asalin jihar Adamawa ce daga Mubi mahaifinta kuma ɗan ƙasar Gabon, ta ce ta ƙara jin ta kamu da matsanaicin son Malamin ne tun bayan wani bidiyonsa da ta kalla yana lacca a jami’ar musulunci dake birnin Madina na ƙasar Saudiyya.

Ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami

Hadiza Gabon wacce ake wa laƙabi da uwar marayun Kannywood, na daga cikin jarumar masana’antar mata attajirai, ta kuma ce ba kuɗin Malamin ne ya ja hankalinta ba, domin a wadace take. Ta shaida cewa a shirye take a kowani lokaci ta daina yin fim idan har Sheikh Pantami zai aure ta.

Jaruma Hadiza Aliyu Gabon

A cikin wani gajeren bidiyon da ta ɗora a shafinta kuma yake yawo a shafukan Instagram da Facebook, ta yi alƙawarin zama mace tagari, mai addini da bin ƙa’odojin mijinta har da zama matar kulle idan Pantami ya buƙaci hakan.

Ta ce bata da wani babban buri a yanzu da ya wuce ta yi aure ta haifi ƴaƴa kuma Sheikh Pantami ne burinta kuma shi take ta yin mafarkin ta zama matarsa a ƴan kwanakin nan.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan