Shekaru 34 da ƙirƙiro jihar Katsina: Jihar da kalubalen tsaro ke ƙoƙarin kai ta ƙasa

708

Haƙiƙa tun da aka ƙirƙiro jihar Katsina daga tsohuwar jihar Kaduna a ranar 23 ga watan Satumbar shekarar 1987, jihar ta samu ci gaba mai ɗorewa a ɓangarori daban-daban.

Haka kuma jihar Katsina ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da ake da su a arewa maso yammacin Najeriya, inda ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar. Bugu da ƙari jihar Katsina ɗin dai tana ɗaya daga cikin jihohin da suka samar da shugabannnin ƙasa wanda suka haɗa da marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua da shugaban ƙasa mai ci Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari da Sarkin Katsina Abdulmumin Usman da kuma Gwamna Aminu Bello Masari

Sai dai a lokacin da Katsinan ke murnar cika shekaru 34 da kafuwa, jihar na fama da matsalolin tsaro da ake alakantawa da ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, wanda hakan ke matukar barazana ga tattalin arzikin jihar musamman ta fuskar noma da kasuwanci.

Duk da cewa mahukunta kan ce suna iya bakin kokarinsu don tabbatar da zaman lafiya a jihar ta Katsina, amma bayanai na nuna yadda ake samun ƙaruwar hare-hare da satar mutane, abin da ke nuni da cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

Domin ko a baya-bayan nan sai da gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya shawarci ƴan jihar da su ɗauki makamai domin kare kawunansu, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Shin Buhari ya yi watsi da jihar Katsina ne?

Jihar Katsina dai ita ce jihar da shugaba Muhammadu Buhari ya fito kuma ta kasance ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya kamar Zamfara da Kaduna da ke fama da matsalolin tsaro da suka danganci fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

Yankuna da dama na jihar na ganin hare-hare a kai a kai inda ƴan bindiga ke aukawa ƙauyuka su kashe mutane sannan su yi awon gaba da mata da ƙananan yara tare da satar dabbobi.

Masu lura da lamuran tsaro sun yi kiyasin cewa waɗannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da raba dubbai da gidajensu.

Sai dai a ƙoƙarin da fadar shugaban kasa ke yi na magance kalubalen tsaron, a cikin watan Mayun shekarar 2020 shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron ƙasar nan umarni na ƙaddamar da sabon yunkuri domin kakkabe ƴan bindigar da su ka addabi jama’a a jihar ta Katsina, sai dai a iya cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba domin tuni mazauna jihar da dama suka yanke kauna kan kokarin da jami’an tsaro suke yi na shawo kan matsalar.

Gwamna Aminu Bello Masari

Ko a cikin watan Disambar shekarar 2020 sai da wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar sakandiren garin Ƙanƙara inda daga baya gwamnati ta ceto su.

A ɓangaren gwamnatin jihar wanne mataki ta ke ɗauka akan ƙalubalen tsaron?

A ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata ne gwamnan jihar ta Katsina ya sanya hannu kan dokar Shawo Kan Matsalolin Tsaro da niyyar magance wasu matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar.

Dokar wacce ta fara aiki tuntuni na ƙunshe ne da matakai 12 da suka haɗa da:

 1. Haramta safarar shanu daga jihar Katsina zuwa kowace jiha a Najeriya.
 2. Haramta daukar itace a manyan motoci daga cikin jeji.
 3. Haramta sayar da dabbobi a kasuwannin kananan hukumomin Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Kankara da Malumfashi da Charanchi da Mai’aduwa da Kafur da Faskari da Sabuwa da Baure da Dutsinma da kuma Kaita.
 4. An haramta sayar da baburan da aka taba amfani da su a kasuwar Charanchi.
 5. An hana daukar mutum uku a kan babur daya da kuma daukar fiye da fasinja uku a babur mai kafa uku wato Keke Napep.
 6. Sannan dokar ta ba da umarnin rufe titin Jibiya zuwa Gurbi Baure inda motoci za su daina bi, sai su dinga bin hanyar Funtuwa a maimakonta har sai baba ta gani.
 7. Ita ma hanyar Kankara zuwa Sheme an hana motocin haya bin ta, an kuma ba su shawarar su dinga bin hanyar Funtuwa. Sai dai an bai wa motoci masu zaman kansu umarnin bin hanyar idan suna bukata.
 8. Dokar ta kuma ƙayyade sayar da man fetur inda ba za a sayar wa masu ababen hawa na fiye da naira 5,000 ba a wasu ƙananan hukumomi 12.
 9. Sannan a wasu gidajen mai biyu ne kawai da aka yarda a sayar da man, a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari da Safana da Danmusa da Faskari da Dandume da Musawa da Matazu da Dutsinma da Kurfi da Danja da kuma Kafur.
 10. Sannan kuma an hana sayar da man fetur a jarka.
 11. Kazalika dokar ta jaddada haramta zirga-zirgar babura da keke Napep daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a cikin birnin Katsina, sai kuma daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ƙananan hukumomin jihar.
 12. Sai dai kuma dokar ta bai wa ma’aikatan lafiya da ‘yan jarida da jami’an tsaro damar amfani da babur da Keke Napep a lokutan da aka haramta din.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ɗauki matakin toshe layukan sadarwa a wasu sassan jihar ta Katsina. Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da Ɗanmusa.

Wani yaro mai kimanin shekaru 10 a yankin ƙaramar hukumar Safana da matsalar tsaro ta tilasta shi shiga bijilanti

Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da Ɗandume.

Jihar Katsinan da ta yi shuhura a ɓangaren iya tafiyar da mulki da kuma ilimi har ta kai ana yi mata kirari da ta “Ta Dikko Ɗakin Kara”, amma a yau rashin tsaro yana ƙoƙarin durkusar da wannan jiha mai dimbin tarihi!

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan