A daidai lokacin da wasu daga cikin ƴan Najeriya ke yiwa jami’an ƴan sandan kallon waɗanda ba sa godiya da abin da gwamnati ta ke ba su na albashin su a duk ƙarshen wata saboda yadda wasu daga cikinsu su ka yi ƙaurin suna wajen karɓar cin hanci da rashawa.

Sai ga shi wani jami’in ɗan sanda ɗan asalin jihar Katsina mai suna Mohammed Iliyasu Kurfi mai muƙamin SP, ya kasance yana rabawa masu ƙaramin karfi albashinsa domin agaza musu.
SP Mohammed Iliyasu Kurfi, ya shiga aikin ɗan sanda ne da muƙamin ASP inda a cikin shekarar 2010 ya fara aiki da rundunar ƴan sanda ta ƙasa shiyyar jihar Yobe, kafin daga bisani a mayar da shi birnin tarayya Abuja.

Tun da farko hoton bidiyon wannan jami’in ɗan sanda yana rabon kuɗi haɗe da wani rubutu da ke bayyana cewa albashinsa ya ke rabarwa ya karade shafukan sadarwa na zamani inda ya ke samun yabo tare da jinjina daga ƴan Najeriya.
SP Mohammed Iliyasu Kurfi dai a halin yanzu shi babban baturen ƴan sanda wato DPO a karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina.

Aikin ƴan sandan Najeriya, kamar sauran ƴan sanda a duniya aiki ne mai matuƙar muhimmanci na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp