Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya ta musanta rahoton nadamar goyon Buhari

407

Kakakin kungiyar dattawan arewacin Najeriya Dr Hakeem Baba Ahmed ya musanta wasu rahotanni da jaridun kudancin ƙasar su ka rawaito akan cewa kungiyar dattawan ta yi nadamar goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen shekarar 2015.

Dr. Hakeem Baba Ahmed ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook a jiya Alhamis kwana ɗaya da bullar rahoton.

Waɗansu jaridun kudu na ta watsa karya cewa ƙungiyar dattawan arewa ta yi da-na-sanin goyon bayan Buhari a maimakon Jonathan a zaben 2015. Mun dai so a ce Buhari yayi ƙoƙarin yabo, ba gazawar cika alkawuran sa ba. Allah Ya raba mu da masharranta

Martanin na Dr. Hakeem na zuwa ne kasa da mako ɗaya da ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zaɓen wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ƙasar a zaben 2023.

Ƙungiyar ta mayar da martani ne ga matakin da ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya da wasu ƙungiyoyi suka ɗauka cewa lokaci ya yi da mulki zai koma bangarensu.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan