Shekaru 16 da rasuwar Dokta Yusuf Bala Usman: Mutum mai kishin talakawan Najeriya

  1019

  Dokta Yusuf Bala Usman mutum ne basarake, mashahurin malami masanin tarihi da kimiyyar siyasa, dandaƙaƙƙen marubuci, ɗan kishin ƙasa, mai fafutikar ƴanci, haziƙi kuma fasihi, sannan kuma maras tsoro.

  Tabbatas, babu tantama bare kokwanto cewa, wannan bawan Allah ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen wayar da kan jama’a, haɓɓaka ilimi, irin wacce ta dace a kuma daidai lokacin da ya da ce.

  Wannan bawan Allah ya tafiyar da rayuwarsa kacokaf, wajen karantarwa, fafutikar ‘yanci da ganin an tabbatar da adalci, da kuma bayyana tarihi. “Dr. Bala Usman Tekun bayanai (ilimi) ne. Nitsatten manazarci, shi ne Dr. Bala Usman wanda ke da kundayen a kowanne fanni da kuma kowane irin mutum. Idan baka taɓa bashi kwafin muƙalarka ba ko wani abu da ka wallafa, to shi yana da kundin a kanta. Idan kana neman ƙarin bayani a game da wani fanni, to ka tambaye shi. idan bashi da ta cewa, to zai gaya maka gurin da za ka samu kai tsaye.

  An haifi Yusuf Bala Usman a garin Musawa ta jihar Katsina, a cikin watan Mayun shekarar 1945. Dr. Yusuf Bala Usman jini sarautar Katsina ne. Shi ɗan Durbin Katsina ne, kuma ɗan’uwan Sarkin Katsina Usman Nagogo. Haka nan kuma shi jikan sarkin Kano Abdullahi Bayero ne ta wajen mahaifiyarsa.

  Dr. Yusuf Bala Usman ya fara karatunsa na firmare a ‘Musawa Junior Primary School’ daga shekarar 1951 zuwa 1954, sai kuma ‘Kankia Senior Primary School’ daga shekarar 1956 zuwa 1957, daga nan kuma sai ‘Government College Kaduna’ daga 1958 zuwa 1962.

  Dr. Yusuf Bala Usman a ƙasashen waje ya zurfafa karatunsa. Ya halarci ‘Uniɓersity Tutorial College’ da ke Great Russell Street, Landan, daga shekarar 1963 zuwa 1964. Sannan kuma ya shiga ‘Uniɓersity of Lancaster’ da ke Landan, inda ya fita da digiri a fannin tarihi da kimiyyar siyasa (Bachelor of Arts (Hons) in History and Political Science), daga shekarar 1964 zuwa 1967.

  Marigayi Dokta Yusuf Bala Usman

  A Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya yi karatunsa na digiri na biyu da kuma digirin digirgir daga shekarar 1970 zuwa 1974.

  Bayan dawowarsa gida Najeriya, Dr. Bala Usman ya fara karantarwa a Kwalejin Barewa (Barewa College) da ke Zariya, tun daga shekarar 1967 har zuwa 1971. Daga baya ya fara Koyarwar wucin gadi (Part Time Lecturing) a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kafin daga baya ya zama malami na dindin. Wannan shi ne aikin da yake kai har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

  Ya Riƙe muƙamin shugaban sashen tarihi daga 1979 zuwa 1980, sannan kuma ya riƙe muƙamin Mataimakin shugaban Tsangayar darrusan ‘Art’ da kimiyyar hulɗatayya (Deputy Dean, faculty of Arts and Social Science) a 1977, sannan kuma shi mamba ne a majalisar sanatocin jami’a (member university senate) tun daga 1976 har zuwa 1980.

  Yusuf Bala Usman ya zama mamba na masu shifter kundin tsarin mulkin Najeriya (minority submission members of the constitution drafting committee) daga shekarar 1975 zuwa 1976. Sannan ya zama mamba na kwamatin sabunta Ƙa’idojin Hulaɗa da Ƙasashen Waje na Najeriya (Nigeria’s foreign policy) daga 1975 zuwa 1976. Sannan kuma ya zama mamba na jakadun Najeriya zuwa ƙasar Angola a shekarar 1976. Sannan kuma ya zama mai bada shawara na musamman ga Wakilcin Najeriya ga zaman musamman na 31 da na 41, da zauren majalisar Amurka ya gabatar (special adɓiser to the Nigerian delegation to the 31st and 41st special sessions of the United Nation’s General Assembly) a shekarun 1976 da 1986.

  Haka nan kuma yana cikin kwamatin amintattu na ƙungiyar ƙwadagon Najeriya (NLC) tun daga 1978 har zuwa 1980, kuma ya zama ko-odinato na kwamatin karɓar mulkin Jahar Kaduna a shekarar 1979, sannan kuma daga baya ya zama sakataren gwamnatin jahar Kaduna a lokacin gwamna Balarabe Musa daga shekarar 1979 zuwa 1980. Ya zama darektan nazari na jama’iyyar PRP daga 1979 zuwa 1980. Da sauran abubuwa da ya riƙe masu tarin yawa.

  Dr. Yusuf Bala Usman, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimi da kuma bunƙasa shi, kamawa tun daga rubuce-rubuce har zuwa kan buɗe cibiyoyin nazari. Ya rubuta takardun da Allah kaɗai ya san iya yawansu. Gudunmawar da Bala Usman ya bayar ta fi ƙarfin rubuce-rubucen da ya yi ya bari saboda ƴan baya.

  Ta wannan hanya ta rubuce-rubuce, Allah ne kaɗai ya san mutanen da suka zama ‘yan kishin ƙasa. “Bala da abokansa malamai ‘yan fafutikar ‘Yancin Ɗan’adam a faɗin Nahiyar Afirka, waɗanda suke karantarwa a jami’o’i da dama a Najeriya a wancan lokacin da man fetur ya ɗauki hankalinmu, sun farkar da mu tare da haskaka mana fitilar cewa lallai za mu iya canzawa zuwa ga rayuwa mai inganci.

  Akwai mashahuran mutane waɗanda kai tsaye ko a fakaice sun tasirantu da rayuwarsa, “Duk da cewa, da yawa daga cikinmu waɗanda suka san Bala tun yana ƙarami, za su yi matuƙar jin nauyin wannan rashi na malaminmu kuma ubangidanmu, sannan kuma babanmu, masaninin tarihin gida da ƙasashen waje”.
  Daga cikin irin mutanen da suka tasirantu da rayuwar tasa akwai mutane irin su Hadiza Bala Usman wacce take ‘ya a gareshi, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, Tajuddeen Abdur-Raheem, da sauran jama’ar da sanin su sai dai Allah. “Ba za a manta da wannan haziƙin malami ba, saboda mutum ne da ya ce bai yarda da zaluntar talakawa da ake yi ba.

  Haka nan ya rubuta takardun da ba za su ƙirgu ba dangane da haɗin kan Najeriya. “Dr. Usman ya ƙware wajen fito da haɗɗuran da ke tattare da rarrabuwa, a kuma daidai lokacin da ƙasashen duniya suke yunƙurin haɗewa ƙarƙashin ƙungiya ɗaya.

  Yusuf Bala Usman ya rasu a ranar Asabar 24 ga watan Satumba na shekarar 2005.

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan