An tabbatar da Khalifa Muhammad Sanusi II a matsayin uban jami’ar KASU

615

A yau Lahadi hukumomin jami’ar jihar Kaduna wato KASU su ka tabbatar da tsohon Sarkin Kano kuma Khalifan Tijjaniya na Najeriya, Malam Muhammad Sanusi II a matsayin uban jami’ar.

Tabbatar da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin uban jami’ar ya zo ne bayan kammala bikin yaye ɗalibai karo na huɗu da ya gudana a jami’ar.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Maris ɗin shekarar 2020 ne Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bai wa Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mukamin Uban Jami’ar jihar Kaduna.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan