Marigayi Sarkin Gaya mutum ne mai halin dattaku – Abba Kabiru Yusuf

1138

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2015 Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya bayyana marigayi mai martaba Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir III a matsayin mutum mai kyakkyawar tarbiyya da kuma gudun duniya.

Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyyar ga masarautar Gaya bisa rashin Sarkin su a makon jiya.

Injiniya Abba Kabiru Yusuf a lokacin ziyarar ta’aziyyar Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir

Haka kuma Abba Kabiru Yusuf ɗin ya yi addu’ar neman rahamar ubangiji ga marigayin.

A ranar Larabar makon jiya ne Allah Ya yi wa Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir rasuwa bayan ya yi fama da doguwar jinya.

Sarkin ya rasu yana da shekara 91, kuma ya shafe shekara 30 yana kan karagar mulki.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan