Rana Zafi Inuwa Ƙuna: Yaushe Najeriya za ta gyaru?

216

Najeriya ce ƙasa ta shida mafi arzikin man fetur a duniya banda dimbin albarkatun ma’adanan ƙasa da Allah ya baiwa ƙasar nan. To sai dai kusan kullum talakawa na daɗa talaucewa yayin da masu kuɗi kuma su ke ƙara kuɗancewa.

Baya ga wannan kuma Najeriya na daga jerin cikin ƙasashen da cin hanci da rashawa ya kassara abubuwa da yawa, inda ake zargin cewa cin hancin ne ya sa matsalolin da ke faruwa a ƙasar nan ke ƙara ta’azzara.

A ɗaya ɓangaren kuma ƙasar na fuskantar mummunar matsalar tsaro da ke addabar Najeriya, akwai tarin matsaloli kama daga na dimbin rashin aikin yi da kuma talauci da ya yi wa al’umma katutu.

Haka kuma natasalar tsaro na ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar, inda a yanzu ana iya cewa babu wani yanki da ya tsira daga barazanar tsaron. Kama daga ƴan ta’addar Boko Haram da ke yankin Arewa maso Gabas, zuwa ga ƴan bindiga da masu garkuwa da suka yi kaka gida a yankin Arewa maso Yamma da ma Arewa ta Tsakiya.

Wasu daga cikin ƙarin matsalolin da al’ummar Najeriyar ke fama da su sun hadar da ɗimbin talauci da yunwa da kuma rashin aikin yi da ma rashin wadatattun hanyoyin kula da lafiyar al’umma. Wadannan abubuwa dai masana na ganin suna da alaka wajen karuwar ayyukan na ta’addanci da ya yiwa ƙasar nan katutu.

Baya ga waɗannan matsaloli ma, akwai batun rashin haskekn wutar lantarki, wanda hakan ke dakile ci-gaban masana’antu da kuma ke taka rawa wajen matsalar rashin aikin yi musamman ga matasa. Fannin ilimi ma ba a barshi a baya ba wajen fuskantar matsala.

A ɓangaren tattalin arziki kuwa wani rahoto da Bankin duniya ya wallafa a cikin watan Nuwambar shekarar 2020, bayyana cewa ya tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma mafi muni a cikin shekara 36.

Hakazalika farashin dalar kullum ƙara tashin gwauron ya ke yi inda a cikin wannan watan na Satumba farashin Dalar ya kai tsakanin naira 572 zuwa 575 a sassan Najeriya, wanda hakan ke haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

Babban burin ƴan Najeriya dai shi burin ganin ranar da za a wayi gari babu waɗannan matsaloli da su ka zame mata kadangaren bakin tulu.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan