A dai-dai lokacin da ya rage ƴan makwanni jam’iyyar APC ta gudanar da zabukan shugabancin jam’iyyar a matakin jihohi a faɗin Najeriya, wasu rahotanni daga fadar gwamnatin Kano na bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na shirin juyawa shugaban riƙon jam’iyyar APC Abdullahi Abbas da ke sake neman wa’adin shugabancin jam’iyyar a karo na biyu baya.
Wata majiya daga fadar gwamnatin Kanon ta bayyana cewa tun kafin Gwamna Ganduje ya tafi ƙasar Birtaniya wajen bikin kammala karatun ɗan sa Muhammad, ya yanke shawarar goyon bayan Mukhtar Ishaq Yakasai ɗin a matsayin shugaban jam’iyyar APC, bayan wata ganawar sirri da ya yi da ƴan majalisu da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Haka kuma majiyar ta ce mafi yawa daga cikin ƴan majalisar dokokin da na wakilai na jihar Kano, da ƴan majalisar dattawa guda uku sun nuna rashin goyon bayansu ga Abdullahi Abbas ɗin akan buƙatar sa ta neman shugabancin jam’iyyar a karo na biyu.
Kamar yadda jaridar Labarai24 ta rawaito cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana goyon bayan kwamishinan ayyuka na musamman kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano da KewayeMukhtar Ishaq Yakasai, domin zama sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.

Bisa wannan dalilin ne Abdullahi Abbas ya kafa wani kwamiti karkashin shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Fa’izu Alfindiki na bayar da haƙuri tare da neman haɗin kan ƴan jam’iyyar da aka bata musu a fadin jihar Kano.
Sai dai kwamitin na fuskantar tirjiya daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin domin tuni su ka yi watsi da wannan kwamiti tare da nuna goyon bayansu ga Mukhtar Ishaq Yakasai ɗin.
Sai dai a lokacin haɗa wannan rahoton mun tuntubi Abdullahi Abbas ɗin domin neman ƙarin bayani sai dai bai ɗauki kiran da wakilinmu ya yi masa.
Abdullahi Abbas wanda ake masa lakabin ‘Ɗan Sarki Jikan Sarki’, shi ke riƙe da shugabancin jam’iyyar APC tun a cikin shekarar 2017, kuma ya daɗe yana furta kalaman da ka iya haifar da rikici wanda al’ummar jihar Kano da ma Najeriya ke ƙalubalantarsa.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp