Abdulsamad Isyaka Rabiu ya baiwa Sarkin Kano kyautar mota ta miliyoyin Naira

1199

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan ɗan asalin jihar Kano, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA, ya baiwa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kyautar motar alfarma da manyan Sarakuna ke amfani da ita ƙirar ‘Rolls Royce Phantom 2021’, wacce darajarta ta wuce Naira Miliyan 200.

Rolls Royce Phantom 2021

Tun da farko shafin masarautar Kano ne ya wallafa hoton bidiyon motar a jiya Asabar tare da gajeren wani rubutu “Allah ya sa abokiyar arziki ce”.

Rolls Royce Phantom 2021

Sai dai wata majiya daga fadar ta tabbatarwa da jaridar Labarai24 cewa ɗan kasuwa Abdulsamad Isyaka Rabiu ne ya baiwa Sarkin kyautar wannan mota ta alfarama.

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Maris ɗin shekarar 2020 gwamnatin jihar Kano ta naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano bayan sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Haka kuma Aminu Ado Bayero shi ne sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan