Masarautar Argungun ta naɗa Lai Mohammed kakakin Kebbi

590

A yau Lahadi Masarautar Argungun da ke jihar Kebbi a Najeriya ta naɗa ministan yaɗa labarai da al’adu na ƙasa Alhaji Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi.

Nadin sarautar ya biyo bayan amincewa da majalisar masarautar ta Argungun karkashin mai martaba Sarkin Argungun Alhaji Sama’ila Mera.

Lokacin da ake naɗa Lai Mohammed Kakakin Kebbi

Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin na Argungun ya ce an ba wa ministan wannan sarautar ne saboda “jajircewa da ƙarfin hali wajen nuna hoton Najeriya a gida da waje ”.

Alhaji Sama’ila Mera ya ce masarautar ta karrama ministan da mukamin ne a matsayin nuna godiya ga kokarinsa na inganta bikin kamun kifi da al’adun Argungu don samun matsayin duniya.

Haka kuma Sarkin na Argungun ya kuma yaba wa tsoffin ministocin al’adu da yawon bude ido kan kokarin da suke yi na inganta bikin a kasa baki daya tun shekarar 1970.

Kakakin Kebbi Lai Mohammed

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan