Muddin Buhari zai nemi zango na 3 zan sayar da ‘Gonata da Gidana’ in ba shi gudummawa – Matashi A Kano

5296

A daidai lokacin da mafi yawan Ƴan Najeriya ke bayyana suƙewa akan mulkin shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC sakamakon yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ƙazanta a arewacin ƙasar nan da kuma yadda ake ƙara fuskantar matsin rayuwa, sai ga shi wani matashi a yankin ƙaramar hukumar Rano da ke jihar Kano yana iƙirarin sayar da gonarsa da gidansa domin taimakon shugaba Buharin muddin zai ƙara buƙatar zangon mulki a karo na uku.

Matashin mai suna Isyaku Ila Ahmad mai kimanin shekaru 32 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin jaridar Labarai24 a ƙarshen mako.

Isyaku Ila Ahmad ya ce haƙiƙa shi dai a tarihin shugabannin da su ka mulki Najeriya babu wanda talaka ya amfana tare da jin dadi tamkar shugaba Muhammadu Buhari.

Matashi Isyaku Ila Ahmad a gonar da ya ke ikirarin sayarwa

“Tabbas ƴan Najeriya sun ga sauye – sauye a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karɓi ragamar mulkin kasar a shekarar 2015, domin a wannan shekarar mu manoma mu ka amfana ƙwarai da gaske sakamakon farfaɗo da darajar noma da gwamnatin APC ta yi”
“Mun samu tallafin noma wanda gwamnatin shugaba Buhari ta fito da shi kuma mun yi amfani da shi yadda ya kamata”

Ya ƙara da cewa “Da za a ce tsarin mulkin Najeriya ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar yin wa’adin mulki zango uku to babu shakka da zan sayar da gonata da gidan da na ke ciki domin baiwa shugaba Buhari gudunmuwar kuɗin gonar da gidan”
Haka kuma Isyaku Ila Ahmad ya bukaci ƴan Najeriya da su cigaba da yiwa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari addu’a da kuma haɗin kai.

“Tabbas ba za a ce shugaba Buhari ya yi daidai a ko ina ba domin fadar hakan kuskure ne, amma tabbas ya yi abin a yaba kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu”

Gidan Matashi Isyaku Ila Ahmad

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan da ma Shugaba Buhari sun karbi mulki ne a shekarar 2015 bayan sun kayar da Shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi ne karon farko da jam’iyyar hamayya ta kayar da mai mulki a tarihin Najeriya.

Haka kuma a wancan lokacin, ‘yan kasar nan na kokawa kan matsaloli daban-daban da suka hada da rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan Boko Haram da tsadar rayuwa da kuma cin hanci da rashawa.

Sai dai bayan kwashe fiye da shekara shida da gwamnatin Buhari tana mulki, ‘yan kasar nan na ci gaba da korafi musamman kan yadda suka ce an samu karin tabarbarewar harkokin tsaro, da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da makamantasu.

Turawa Abokai

6 Sako

  1. Shugaba buhari ya karbi najeria talaka yana rayuwa cikin sauki talaka zaiyi cefenen kayan abinci da kudi Dan kalilan amma yanzu anaji ana gani komai sai famar fin karfin talaka yake

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan