Hoton Motar da ake ji-ta-ji-tar Shugaban Kamfanin BUA ya Bawa Sarkin Kano, Mai Kimar Kuɗi Miliyan 200

413

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya gwangwaje da dalleliyar mota ta alfarma ta gani a faɗa.

Majiyoyi daga Fadar Masarautar Kano sun tabbatar da isowar motar Fadar Sarkin Kano.

Motar ƙirar Roll-royce Phantom, shigen irinta ce Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammadu Sunusi na II yake hawa tun bayan hawansa da sauƙa daga Karaga har zuwa yau.

Roll-Royce Phantom wadda darajar ta ke kaiwa daga Dalar Amurka $455,000 zuwa $535,000, idan aka yi lissafinta a Naira za ta kai Naira miliyan N187mn zuwa N219.8mn (a farashin Dala na Banki). ku karanta:Masarautar Argungun ta naɗa Lai Mohammed kakakin Kebbi

Motar Miliyan Ɗari 2 da aka baiwa Sarkin Kano

Duba da tashin darajar Dala a halin yanzu a kasuwar bayan fage, darajar Dala miliyan $455,000 zuwa 435,000 ta kai; Naira N259 zuwa N304mn. jaridar Dailynigerian sun tabbatar da hakan.

To sai dai Kacallan Kano, Alhaji Magaji Galadima, kuma ɗaya daga cikin hakiman Sarki ya ƙaryata wannan batu da ake ta ya ya tawa inda ya rubuta a shafin sa na Sada Zumun ta cewa “Sabuwar motar Sarkin Kano ba BUA ko Ɗantata ne suka bashi ba kamar yadda ake bazawa”.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan