Zamu taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro a Najeriya – Magoya bayan Abdulaziz Yari

395

Wata ƙungiya mai suna Concerned Citizens of Like Minds (CCLM) a cikin jam’iyyar APC ta yi alƙawarin samar da wasu hanyoyin da za su taimaka wajen ganin an shawo kan matsalar tsaron da ta addabi wasu daga cikin yankin arewacin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar Kwamared Auwal Ɗalhatu Sani ne ya bayyana haka a gurin wani gangamin nuna goyon bayan ga tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar akan kudurinsa na neman shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa da ya guda a Kano.

Kwamared Auwal Ɗalhatu ya ce lokakaci ya yi da ya kamata a ce sun jaddada ƙudirin su na samar da wata runduna da za ta kawo karshen dukkanin wasu abubuwan da su ka jawo matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan dama yankin Arewa.

Haka kuma shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa ba komai ne ya kawo su Kano ba illa yin mubayi’a tare da nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar.

Wani ɓangare na magoya bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar

” ‘Kyakkyawan ƙudirinsa da jajircewar sa lokacin da ya na shugabancin jihar Zamfara ya sanya mu muka nuna goyan bayan mu a gareshi kuma hakan ne ya bashi damar ɗaukar tsawon lokaci yana aiki a matsayin shugaban gwamnonin ƙasar nan”, a cewar Ɗalhatu Sani

A lokacin taron gungun matasan sun taɓo wasu matsalolin da su ka zamar wa matasan arewancin ƙasar nan alaƙaƙai wanda ya ce ya kamata a ce an kawo ƙarshen hakan.

“Haɗuwar mu za ta kawo kakkyawan sakamako ga wannan ƙasa tare da sanya gwaraza a gaba wajen ganin sun ceci jihar mu da ma kasar mu”.

“Muna kira ga jam’iyyar APC mai mulki da ta duba ɗan kishin ƙasa kuma gwarzo abin koyi wajen ganin an ba shi goyon baya wajen kaiwa ga nasarar samun muƙamin Shugabancin jam’iyyar”

A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga shuganni da cewa ako da yaushe su kasance masu yin la’akari wajen samarwa da matasa hanyoyin cigaban su kamar samar musu da ingantacciyar hanya da za su tsaya da ƙafar su da ma samun kwanciyar hankalin wannan ƙasa baki ɗaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan