Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau na cigaba da wallafa hotunan ta tare da wasu jaruman fina – finai a masana’antar Bollywood da ke ƙasar India a shafinta na Instagram.

Tun a cikin farkon watan nan na Satumba masu amfani da shafukan sada zumunta musamman waɗanda su ke bin diddigin rayuwar fitacciyar tauraruwar Kannywood ɗin su ka fara wallafa hotunan ta a ƙasar Indiya tare da bayyana ra’ayoyi mabambanta bayan da ta isa ƙasar.
Jarumar Kannywood ɗin dai ta isa ƙasar ne domin fara fitowa a wani sabon fim na Bollywood mai suna Khuda Haafiz.

Sai dai wani abu da ke baiwa al’umma mamaki shi ne yadda jarumar ta rikide ta koma tamkar Ba – Indiya domin a duk hotunan ta da ta wallafa sun yi matuƙar sajewa da sauran jaruman na Bollywood.
Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2015 Rahma Sadau ta fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya da aka fi sani Nollywood, inda ta fito a cikin wani shirin fim mai suna ‘The Light Will Come’.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp