Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tsayar da kowace ranar 28 din watan Satumba a matsayin ranar samun bayani ta duniya.
Najeriya na cikin kasashen duniya da aka tsayar da dokar samun bayanan gwamnati ko kuma jami’an tsaro.To sai dai ba kasafai ba ne jami’an gwamnati ko na tsaro ke bin umarnin kotu ba dangane da bada bayanai.
Sau tari hakan ƴan jarida ko lauyoyi na samun bayanai daga hukumomin gwamnati ba ya cimma ruwa.
Sai dai masana kan harkokin sadarwa na kallon ƴan jarida ma basu ba ranar wani mahimmanci ba ta hanyar yin gangami ko shirya ƙasidu akan yadda hukumomin gwamnati su kan ki su bayar da rahoton da ake nema.

Haka kuma ƴan jarida na fuskantar matsaloli a Najeriya wajen tara bayanai saboda ɗari – ɗari da jami’an gwamnati ke yi da ƴan jarida. Idan kuma su jami’an gwamnatin suna wata muna-muna ba za su so ba da bayani ba.
Sai dai dokar bayar da bayanai ta bayyana cewa duk wani dan kasa nada ƴancin ya nemi bayani daga gwamnati ba tare da gindiya masa wasu sharuda ba, kuma dokar ta baiwa ƴan ƙasa damar zuwa kotu domin tilastawa ma’aikatar gwamnati akan ta bayar da bayanan da mutum ke nema.
Hakazalika akwai hukuncin daurin shekara daya ga duk jam’in gwamnatin da yaki bada bayanan da ake nema, kuma duk wani jami’in gwamnati da ya ga ana almundahana ya kuma bayyanawa jama’a doka ta kareshi daga duk wani hukumci.
A ƙarshe sashen dokar ya yi umarnin cewa a cikin kwanaki bakwai a baiwa mutum bayanan da ya bukata, idan kuma ba’a bayar ba to a ba da cikakken bayanin dalilin da ya sa ba’a yi ba cikin kwanaki bakwan.
A cikin shekarar 2015 hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta amince da ranar 28 ta kowane watan Satumba a matsayin ranar samun bayanai ta duniya.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp