Gwamnatin Jihar Kaduna na dab da Katse Layukan Sadarwa – El-Rufa’i

362

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da al’ummar jiharsa cewa su shirya domin za a katse layukan sadarwa a ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na ƙaddamar da hari kan ‘yan bindiga da ke ɓuya a wasu ƙananan hukumomi.

Gwamna El-Rufai ya ce katse layukan ba zai shafi duk jihar ba, amma wasu sassan na jihar kamar ƙananan hukumomin da ke iyaka da Zamfara da Katsina za a katse layukansu.

Elrufai ya ce katse layukan da aka yi a jihohin Zamfara da Katsina ya bai wa ‘yan bindiga damar kutsa kai wasu ƙauyukan makwabtan jihohi kamar Kaduna domin amfani da layukan waya don amsar kuɗin fansa.

Ya ƙara da cewa tuni ya aike wa gwamnatin tarayya wannan buƙata wanda ya ce shugaba Buhari ya amince da matakin. Ku karanta:Ranar Yancin Bayanai: Cibiyar CITAD ta shirya liyafar cin abinci da ƴan jarida a Kano

Yankunan Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kajuru da Kachia su ne suka fi fuskantar barazana daga hare-haren ‘yan bindiga.

Sannan gwamnan ya ce tuni gwamanati ta kaddamar da rundunar kar-ta-kwana da za ta ke zagaye a kowanne sassa domin tabbatar da cewa mutane na bin dokokin da aka kafa domin daƙile ‘yan bindiga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan