Yadda Ta Kaya A Gasar Kofin Zakarun Nahiyar Turai Wannan Makon

405

Ƙwallon da Federico Chiesa ya ci a cikin daƙiƙaa 10 daga dawowa hutun rabin lokaci ya sa Juventus ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar zakarun Turai.

Cristiano Ronaldo ya zira ƙwallo a mintin ƙarshe wanda yasa Manchester United ta doke Villarreal a gasar rukunin F na gasar zakarun Turai.

Barcelona ta sha kashi a hannun Benfica da ci 3-0, tun bayan shekarar 1997 wannan shi ne karon farko da ta yi rashin nasara a wasa biyar a gasar zakarun Turai.

Robert Lewandowski ya zira ƙwallaye biyu inda Bayern Munich ta yi nasara akan Dynimo kyiv, Munich ta yi nasara a wasanta biyu a gasar zakarun Turai.

Ɗan wasan Leicester City, Kelechi Iheanacho ba zai buga wasunsu da Legia Warsaw ba a gasar Europa saboda wata matsala da takardun tafiyarsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan